Mayakan Ansaru Na Auren Ƴan Mata A Jihar Kaduna

Daga BBC Hausa

Rahotanni daga yankin Birnin Gwari a Jihar Kadunan Najeriya na cewa ƴan ƙungiyar Ansaru na ƙulla aure tsakanin ‘yan matan yankin da mayaƙanta.

Irin wannan lamari dai ya faru a garin Tsohuwar Kuyallo, inda wasu ‘ya’yan ƙungiyar suka angwance da ‘yan matan garin a ranar Talata.

Wani mazaunin yankin Birnin Gwari ya tabbatar wa BBC da ɗaurin auren, inda ya ce ba sabon abu ba ne a yankin.

Ya kara da cewa ko a watanni kimanin biyu da suka gabata mayaƙan ƙungiyar sun haɗa aure da wasu ‘yan mata biyu a yankin.

BBC ta tuntuɓi rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna game da wannan lamari, inda ta ce tana gudanar da bincike a kai.

Sai dai masana harkokin tsaro kamar Muhammad Kabir Isa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, na ganin sakacin gwamnatin Najeriya ne ta fuskar tsaron ya sa kungiyar ke amfani da irin wadannan hanyoyi domin samun shiga tsakanin al’umma, har abin ya kai ga hada zuri’a.

“Yanzu idan suka yi aure cikin jama’a, yaran gidan ko mazan da ke ciki sun zama nasu, waɗannan duk dabaru ne na samun mabiya da mutanen da za su dauki akida da ra’ayoyinsu,” in ji Muhammad Kabir.

Ya bayyana cewa kulawar da gwamnati ta gaza bayarwa ne har ya sa ƙungiyoyi kamar Ansaru ke shiga cikin al’ummomi domin ba su tallafi domin jawo ra’ayinsu.

Yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna na daga cikin yankunan da kungiyoyin tayar kayar baya suka addaba.

Yanki ne da a tsawon shekaru yan fashin daji ke kai hare-hare a garuruwa da kuma kan matafiya a hanyoyi, inda suke kashewa ko garkuwa da su.

Sai dai a baya-bayan nan yankin ya kara shiga tasku, bayan da rahotanni ke ta nuna cewa kungiyar ta Ansaru ta samu gindin zama a nan.

An rika samun bayanai kan yadda suke iko da wasu yankunan na Birnin Gwari, har ta kai ga suke da wuka da nama kan abubuwan da ke faruwa a wasu garuruwan.

Kamar yadda binciken cibiyar Nazari kan tsaro ta ISS ya nuna, Ansaru ta kafu ne a wasu yankunan Arewacin Najeriya Shekaru goma da suka wuce.

Kuma ta samu ne bayan ballewar wasu ‘ya’yan babbar kungiyar Boko Haram, a dalilin rashin jituwa tsakanin masu matsakaici da kuma masu tsatstsauran ra’ayi.

Kuma tun daga lokacin ta rika fadada ta hanyar kulla kawance da kungiyoyin yan bindiga da garkuwa da mutane a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: