Mawaki Rarara ya Buɗe Manhajar Kallon Finafinan Kannywood ta ‘Arewa Cinema’

Daga Ibrahim Hamisu

Shahararren mawaƙin siyasar nan, Kuma shugaban kungiyar 13-13 na kasa Dauda Adamu Abdullahi (Rarara), shi ma ya fito da gidan yana inda za a iya kallon finafinai da waƙoƙin Hausa, da ake cewa ‘streaming’ a turance.

Gidan yanar nasa mai suna  ‘Arewa Cinema’ shi ne na uku irin sa da aka buɗe, wato bayan Northflix na Jamilu Abdussalam da kallo.com na Maijidda Modibbo.

Mai taimaka wa Rarara a fagen soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya tabbatar wa da mujallar Fim cewa lallai ubangidan nasa shi ne mamallakin manhajar ‘Arewa Cinema’, wanda hakan amsa ce ga masu tambayar wane ne ya ƙirƙiro ta kimanin mako biyu tun da aka fara tallata ta a soshiyal midiya.

An kuma dora wasu daga cikin finafinan akan  manhajar ‘Arewa Cinema’. A yanzu haka akwai finafinai da dama a kan manhajar, irin su Mariya, Hafeez, Mujadala, Wutar Kara, Ana Dara Ga Dare, Salmah, da sauran su. Akwai kuma finafinai masu dogon zango irin su ‘Wuff’ da sauran su, sannan akwai waƙoƙi.

Bayanai sun nuna cewa a tsarin biyan kuɗi kafin mutum ya fara kallo a manhajar, a shekara zai biya N9,500, sannan in duk wata ne zai riƙa biyan N1,000 ne.

Haka kuma wakilin mu ya gano cewa su ma masu ‘Arewa Cinema’ sayen fim su ke yi a hannun masu shiryawa kamar yadda sauran su ke yi.

Sannu a hankali dai abubuwa na ƙara faɗaɗa a Kannywood, saura da me? babban ƙalubalen da ke gaban ‘yan Kannywood shi ne su ma a fara ganin finafinan su a Netflix.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: