Mashaya Taba Sigari Kimanin 30,000 Ne Suka Mutu A Shekarar Bara A Najeriya – WHO
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar mummunar illar cututtuka masu nasaba da hayaki inda aka yi asarar rayuka kimanin 30,000 a shekarar 2022.
Wani daftarin rage cutar da taba sigari ta duniya ya nuna cewa kimanin kashi 4.1% na manya a Nijeriya suna shan taba a halin yanzu, wanda ke wakiltar kusan mutane miliyan 4.5 da kashi 7.9% maza ne yayin da mata ke da kashi 0.3% na masu shan taba.
Da yake jawabi a bikin ranar shan taba ta duniya ta 2023, kakakin kungiyar Foundation for Consumer Freedom Advancement (FCFA), Abisoye Micheal, ya ce alkalumman na nuna bukatar gaggawa ga gwamnatin Najeriya ta ba da fifikon dabarun rage cutar tabar sigari (THR) kuma ya bukaci gwamnati ta dauki matakin irin na Samfurin da Kasar Sweden ta dauka a baya.
Ya bayyana cewa, ta hanyar yin amfani da tsarin kasar Sweden, Nijeriya za ta iya share fage ga sauran kasashen Afirka, ta yadda za ta ba da misali wajen rage yawan shan taba da kuma samar da kyakkyawar makoma ga mashaya sigari da ma matasa da ke tafe.
Ya ce gagarumar nasarar da Kasar Sweden ta samu a bayyane yake yayin da take matsowa kusa da zama al’ummar da ba ta da hayaki, ya kara da cewa a cikin shekaru 15 da suka gabata, yawan shan taba a kasashen Turai ya ragu daga kashi 15% zuwa kashi 5.6 cikin dari na ban mamaki, wanda ya mai da shi mafi karancin a duniya.
“Wannan nasarar ba wai kawai tana nuna raguwar shan taba ba amma kuma tana nuna raguwa mai yawa a cikin haɗarin da taba sigari ke haifarwa ga kiwon lafiyar al’ummar Kasar.
Har ila yau hakan ya sanya Kasar Sweden shekaru 17 a gaban burin da Tarayyar Turai ke da shi kamar yadda Wannna ƙididdiga mai ban sha’awa wadda shaida ce ga tasirin hanyar da Kasar ta Sweden ta dauka na rage haɗarin da ke tattare da taba sigari” in ji Micheal.