Masarautar Gombe ta yi rashin Ajiya- Dan takarar gwamnan NNPP ya yi alhini

Daga Danjuma Labiru Bolari Gombe

Dan Takarar kujerar gwamnan jihar Gombe a karkashin inuwar Jam’iyyar NNPP Khamisu Ahmed Mailantarki, ya jajantwa masarautar Gombe da al’ummar Kwami bisa rasuwar Ajiyan Gombe Hakimin Kwami Alhaji Haruna Abdullahi.

Mailantarki, ya aike da ta’aziyyar ce a wata takarda da ya aikewa manema labarai, Inda yace mutuwar Ajiyan Gombe babban rashi ce da za’a jima ba’a manta da ita ba.

A cewar sa Alhaji Haruna Abdullahi, wanda har ila yau shi ne Hakimin Kwami, ya bada gudumawa sosai wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Kwami da ma jihar Gombe baki daya.

Ya kuma ce mutuwar ta haifar da wawakeken gibi a karamar hukumar Kwami dama jihar Gombe wanda zai yi wuyar cikewa.

Ajiyan Gombe dai yana daga cikin masu zaben sarki a masarautar ta Gombe kafin rasuwar sa ya shafe shekara 53 yana Hakimi, kuma ya rasu ne a safiyar ranar Litinin din da ta gabata sakamakon doguwar jinya ya rasu yana da shekaru 94.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: