MARTANI: Gwamna Badaru Mai Yasa Sai Sudan Madadin Jihar Jigawa?
Abin farin ciki ne karɓar shawarwari daga “yan jihar Jigawa wadanda suka damu da ci-gaban jihar.
Gwamnatin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a koda yaushe tana yayata bukatar bata shawarwari da kuma suka mai ma’ana daga duk wani da yake jin yana da gudunmawar da zai bayar domin ci-gabn Jigawa.
Wannan rubutu da mai bada shawara na musamman ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, wato Adamu Muhammad Usman yayi tun da farko ya tabbatar da cewa tsarin da
Gwamnatin Jihar Jigawa tayi domin inganta kiwon lafiya abu ne da ya dace.
Domin karin haske dangane da wasu batutuwa da marubucin ya yi matashiya akan su.
Tambayar sa da yayi cewa mai yasa sai “Sudan madadin jihar Jigawa? “Duk da cewa marubucin ya nuna gamsuwarsa da tsarin kiwon lafiya na Karkashi Gwamnatin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar amsar ita ce. Ba’a iyakance ilimi da bigire ko lokaci ko tazara ko kuma wani wuri. Ilimi abu ne da ake iya samu a kowanne bangare na duniya. Wannan kuma shi ne yasa mutane ke zuwa jihar Jigawa daga sauran wurare, kamar dai yadda al’ummar jihar nan su ma ke tafiya wuri-wuri domin neman wannan haja ta ilimi mai dimbin daraja.
Koyarwar addinin Musulunci ta bukaci neman ilimi zuwa ko ina koda kuwa kasar Sin ne wato Chana.
Duk jami’o’in da ke jihar Jigawa akwai bukatar Jama’ar jihar su tafi sauran wurare domin neman ilimi fannonin rayuwar al’umma mabanbamta.
Kasancewar Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya maida samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya mai rahusa a matsayin daya daga manyan kudirorin gwamnatin sa, haka ne yasa ya dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin tabbatar da cimma wannan kudiri.
Gwamnatin sa ta samar da cibiyar kula da lafiya a kowacce mazaba dake fadin jihar nan da nufin ganin cewa an ajiye likita aƙalla guda daya a kowanne asibiti dake duk mazabun jihar nan.
Hakan ce ta sa a shekarar 2016, gwamnatin jihar Jigawa ta tura dalibai 60 zuwa ƙasar Chana domin su karanci ilimin kiwon lafiya.
An tantance dalibai yadda ya kamata, inda aka tabbatar da cewa sun cancanta kafin a dauke su.
Wadannan dalibai tuni sun kammala karatun su na shekaru hudu, inda yanzu haka suke asibitocin koyarwa daban daban suka samun kwarewar aiki, Kasancewar hakan daya daga cikin sharuddan da ya zama wajibi su cika domin samun shaidar kammala karatun su.
Bayan bincike na tsawon shekaru da jami’an dake da ruwa da tsaki suka gudanar da ra’ayoyin da daliban da iyayensu da sauran hukumomi suka bayyana, gwamnati ta gamsu da tsari da kuma ingantaccen tsarin koyarwa da kasar Chana take da shi wajen koyar da daliban kasashen duniya dake karatu a jami’o’in ta.
Yanzu haka gwamnatin jihar Jigawa ta kammala shirye shirye domin daukar nauyin dalibai mata guda 100 domin su karanci ilimin likitanci a jami’ar ‘yaya mata ta AFHAD dake kasar Sudan.
Wannan ne ya kawo mu ga batun tsarin da gwamnati take bi wajen zabar daliban da za su ci gajiyar tallafin karatu.
Ana gudanar da zaɓen daliban ne a fili ta hanyar tallata shirin a kafafen yada labarai, inda ake buƙatar dalibai ‘yan asalin jihar Jigawa dake karatu a makarantun gwamnati waɗanda kuma suka samu shaidar credits a darussa biyar da suka haɗar da Turanci da lissafi da kuma sauran darussan kimiyya guda uku, wadanda kuma basu fara karatu a wasu jami’o’i dake ƙasar nan ba su mika bukatun su.
Da farko sama da dalibai 2,500 ne suka mika bukatun su kuma suka rubuta jarabawar da aka gudanar da ita a buɗe. Babu wani dalibi da ya yi amfani da sunansa.
Tsarin da aka yi shi ne dukkan daliban sun mika bukatun su ne ta hanyar amfani da lambobin wayar su da kuma lambar shaidar rajistar shiga wurin rubuta jarabawar da aka basu.
An gudanar da jarabawar ne karkashin sanya idanun iyaye da kuma jami’an tsaro, wanda kuma bayan kammalawa daliban ne da kansu suka duba jarabawar.
Cikin dalibai sama da 2,500 da suka rubuta jarabawar, dalibai 300 suka samu adadin maki da ake buƙata. Hakan ya sa aka sake shirya wata jarabawar wadda ta hakane aka samu zabo dalibai guda 100.
A lokacin da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yake jinjinawa dukkan gwamnonin jihar Jigawa da suka gabata bisa gudunmawar da suka bayar wajen bunƙasa jihar nan, a koda yaushe yana alfahari da bin ingantaccen tsari wajen gudanar da aiki.
Kuma sanin kowa cewa yana yin la’akari da abin da ke shigowa asusun gwamnatin jihar Jigawa da kuma tarin bukatun al’umma dake gaban sa.
An kashe kudade Naira miliyan dari uku da tamanin da biyar da dubu ɗari biyar da saba’in da biyar wajen ɗaukar nauyin daliban su 100, kuma an yi amfani da kudaden ne wajen biya musu kudin makaranta da wurin zama da tafiye-tafiye da kudin inshora da kuma sauran bukatu.
Gwamnan ya yarda cewa samar da kwararru a fannin kiwon lafiya zai zama abin tunawa dake da dimbin alfanu ga jihar Jigawa da kuma al’ummarta. Abin tunawa ne da ya cancanci a zuba jari cikinsa.
Habibu Nuhu Kila, Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Kafafen Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a