Malam Inuwa Waya ya kai ziyarar ta`aziya rasuwar Sani Buhari da Muktar Adnan

Daga Aliyu Dangida

Mai neman takarar gwamnan Jahar Kano a zaben 2023 karkashin jam`iyya mai mulki ta APC, Malam Inuwa Ibrahim Waya ya kai ziyarar ta’aziyya bisa rasuwar, Alhaji Sani Buhari (Walin Daura) da Sarkin Ban Kano Alhaji Muktar Adnan Danbatta.

Malam Inuwa Ibrahim wanda ake yiwa lakabi da Waya Raba Gardama kuma Garkuwar Ilimin Kanon Dabo ya samu rakiyar Jagoran matasan Jam`iyyar APC na Jahar Kano, Hon. Saddiku Ali Sango a tafiyar takarar Malam Inuwa Ibrahim Waya a matsayin gwamna.

A yayin ziyarar an gabatar da addu`oi na musamman domin nemawa mamatan biyu Gafara da Rahamar Allah SWA, tare da jajantawa iyalai, `yan uwa da abokan arziki na mamatan.

Malam Inuwa ya bayyana rasuwar dattijo dan kishin kasa dan kasuwa basarake, Sani Buhari da Karimi basaraken gargajiya tsohon ma`aikacin gwamnati, Muktar Adnan a matsayin wani babban rashi ga al`ummar kasa baki daya musamman idan aka yi la`akari da irin gagarumar gudunmawa da su bayar lokacin su na raye.

Ya kara da cewa tarihi ba zai taba mantawa da wadannan mutane biyu ba, kuma za a ci gaba da yi masu addu`ar Allah Ya haskaka masu kabarinsu, tare da bai wa iyalai, `yan uwa da masarautar Kano, Daura da gwamnatin jihar Kano da ta Katsina da Nijeriya baki daya bisa wannan babban rashi da aka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: