Majalisar Dattijai ta Saka Wa’adin Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Najeriya

Daga BBC Hausa

Majalisar Dattijan Najeriya ta bai wa manyan hafsoshin tsaron kasar wa’adin wata hudu su kawo karshen matsalolin tsaron da ke addabar sassan kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta yi wata doguwar ganawa da shugabannin a jiya, duk da cewa majalisar tana hutu.

A baya-bayan nan dai lamarin tsaro ya sukurkuce, al’amarin da ya kai ga wasu ‘yan majalisar yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin bai sauya salo ba.

Majalisar dokoki ta bayyana tsor da damuwarta game da ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar, musamman harin da ƴan ta’adda suka kai kwanan nan a Abuja.

Shugaban majaliar dattijai, Ahmad Lawan, ya kira shugabannin tsaro taron gaggawa a jiya, inda ya lamari ne mai ban tsoro.

A taron, sanatoci sun bai wa shugabannin tsaro shawarwari a kan yadda za a kare Birnin Tarayya da ƙasar gaba daya.

Mafi yawan kwamitocin majalisar dokokin su ma sun gana da shugabannin tsaro akan matsalolin tsaron a Juma’ar da ta wuce don sanin me ake ciki a ƙasar.

Majalisar wakilai ta ce ƴan ta’adda suna barazanar kai hari Abuja inda fadar shugaban ƙasa take, inda suka ce dole hukumomin tsaro su yi maganin masu tayar da ƙayar bayan.

A cikin makonnin da suka wuce, birnin tarayya ya fuskanci barazana daga wurin ƴan ta’adda akan kai hari kan wasu dakarun sojji da gidan yarin Kuje.

A ranar Alhamis ɗin da ta wuce ma, ƴan ta’adda sun kai wa sojojin da ke shingen bincike na Dutsen Zuma mai nisan kilomita kadan daga cikin birnin Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: