Maharan da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari Yobe

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Wasu maharan da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Kararko, Katarko mai nisan kilomita 18 tsakaninsa da Damaturu fadar gwamnatin jihar.


Kamar yadda wata majiya da ke kauyen na Katarko ta shaidawa wakilinmu cewar maharan sun shigo kauyen ne da wajen misalin karfe 9.45am na safe cikin motocin akori kura kirar Toyota Hilux irin wadanda sojojin Najeriya ke amfani da su kimanin guda 6 tare da motar Sulke ta yaki mai dauke da babbar bindigar nan da ake amfani da ita don kakkabo jiragen sama da sauran muggan makaman yaki.


Wani mazaunin ƙauyen na katarko da ya tsere cikin daji domin tserar da rayuwarsa, ya  bayyana cewa yana tsammanin yan ta’addan sun zo satar kayan abinci ne saboda ranar Ƙasuwar ƙauyen na su ne. Shine ya rika jin amon manyan-manyan makaman yaki babu kakkautawa na tsawon lokaci daga bisani ya ji tsit, shine daga nan ya dawo kan hanya ya tari wata mota zuwa Damaturu.

Shi kuwa wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaye sunansa ya ambata cewar lalle maharan sun kwashi kayayyakin abinci da na masarufi sun tafi da su amma kuma da idon sa ya ga dakarun tsaron sojojin dake garin sun bi su wadda yake kyautata zaton za su cimma su.

Wannan hari da maharan su kai garin na Katarko shine hari kusan na biyu da suka kai tun harin 16 ga watan Maris na wannan shekara ta 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: