Mabukata sama da 1,000 sun amfana da rabo zakka na Naira Milyan 4 da Rabi a Jigawa.


Daga Gambo G. Aujara


An raba zakkar amfanin gona ta kimanin naira miliyan 4,412,650 ga mabukata 1,331 a gundumar Gwiwa da ta Dandi dake a yankin masarautar Kazaure.

Shugaban kwamatin zakkah na masarautar Kazaure, Alhaji Bala Mohd ya bayyana haka yayin da ake raba zakkar a gundumar Dandi, ya kara da cewar kwamatin ya raba zakkar kudi naira N110,000 ga mabukata a gundumar Gwiwa.

Shugaban ya bayyana cewar kwamatin ya kammala dukkan tsare-tsaren sa wajen raba zakkar ta wannan shekara a gudumomi 9 dake a yankin masarautar Kazaure.

Makaman Kazaure, Alhaji Jamilu Umaru Adamu ya jaddada aniyar masarautar Kazaure wajen bada gudunmawa a dukkanin aiyukan da ya shafi addinin musulunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: