Lafiya Zinariya: Ramin Hakori Na Janyo Ciwon Zuciya


Daga BBC Hausa

Kwayoyin cutar da ke makalewa a cikin ramin hakori na iya janyo ciwon zuciya, idan ba a dauki matakan da suka dace ba, in ji likitoci.


Hakan a cewarsu, yana daya daga cikin matsalolin da rashin tsaftace baki ke janyo wa.


Kwayoyin cutar dai suna bi ta cikin jini ne, su je har cikin zuciya, su yi wa mutum lahani.


Rashin tsaftar baki kuma na janyo karfin hakori ya yi ta raguwa, har ta kai ana cire su.


Wata matsalar kuma da rashin tsaftace baki ke janyowa ita ce ta warin baki, wanda shi ma ramin hakori na taimakawa wajen kawo shi.


Likitoci sun bayyana karin wasu abubuwan da ke janyo warin bakin da suka hada da yin amfani da tsinken sakace.


Saboda yana kara girman ramin da hakori ke ciki a jikin dasashi, abin da ke sawa abinci ko wasu kwayoyin cuta su makale a ciki.


Wasu dalilan kuma sun hada da dasashi mai jini.


Da numfashi mai wari, wanda gyatsar masu gyambon ciki ke janyowa.


Cin abinci ko abin sha masu karfin kamshi ko masu yaji suma su kan janyo warin baki.


Haka zalika cin kayan zaki kan bata hakori kuma su janyo warin baki.


Sai dai wasu daga cikin muhimman hanyoyin magance warin baki su ne:

Wanke baki sau biyu a rana.

Yin amfani da igiya wajen 

yin sakace maimakon tsinke.

A daina shan sigari.

Zuwa wajen likita domin wanke baki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: