Kwamishinan Matasa na Yobe ya Rasu

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu 

Kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Yobe, Honorabul Goni Lawan Bukar ya rasa ran sa sanadiyyar hatsarin mota da ya rutsa da shi a jiya talata kan hanyar Damaturu zuwa Kano. 

Shi dai marigayi Goni Bukar, wanda aka fi sani da BUGOM, ya yi aiki a matsayin kwamishina a gwamnatin gwamna, Hon Mai Mala Buni bayan da bai samu dacewar komawa ga majalisar wakilai ta kasa ba a 2019 sakamakon maye gurbin sa da aka yi da wani dan takarar. 

Wata majiya ta kusa da iyalin sa ta tabbatar da mutuwar Kwamishinan a wani sakon da aka wallafa a shafinsu na Facebook, da yammacin talata mai taken, “A huta lafiya, Goni Lawan Bukar, BUGOM”.

Ya kasance kwamishinan ma’aikatar filaye, safiyo da  ma’adanai, an zabe shi dan majalisar wakilai mai wakiltar Bursari/Geidam/ Yunusari  kuma ya rike matsayi da dama a kwamitocin dabam-dabam a majalisar wakilai ta kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: