Kungiyar Ci Gaban Makoda Ta Karrama Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Mahmuda Abdullahi

Daga Aliyu M. Dangida

Kungiyar ci gaban Makoda ta karrama shugaban karamar hukumar, Alhaji Mahmuda Abdullahi (Turakin Makoda) da lambar girmamawa tare da wasu muhimman mutane bisa gudunmawar da yake bai wa yankin tun bayan zabensa.

A wata sanarwa da mujallar Mahangar Arewa ta dauko daga shafin babban mataimaki na musamman na shugaban karamar hukumar Makoda akan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Aminu Adamu Ibrahim, yace Shugaban kungiyar, Auwal Sani Isah ne ya gabatar da kambun girmamawar ga shugaban karamar hukumar tare da wasu muhimman mutane da ke yanki wadanda su ka bada tasu gudunmawa wajen ciyyar da karamar hukumar Makoda gaba.

Auwal Sani ya kara da cewar gudunmawar da shugaban karamar hukumar ya bada a fannin ilmi, lafiya da samar da ruwan sha da sauransu abin a yaba ne, musamman idan aka yi la`akari da yadda fannonin suke da amfani tare da taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar al`umma, ya ce wannan ci gaba da Turakin Makoda ya samar ba abin mamaki bane musamman idan aka yi la`akari da cewar matashin dan siyasa ne mai kishi da son ci gaban yankin da al`umma ne.

 A cewar sanarwa “Shugaban karamar hukumar Makoda, Alhaji Mahmuda Abdullahi na daya daga cikin mutanen masu muhimmanci na karamar hukumar wanda aka karrama su da lambar yabo bisa irin gudunmawa da suke badawa a fannoni daba-daban musamman ma ilmi da lafiya”.

A jawabinsa, Shugaban karamar hukumar, Hon Mahmud Abdullahi ya nuna farin cikinsa da jin dadi bisa wannan karramawa da kungiya mai albarka (Makoda Development Association) ta yi masa, inda yayi alkawarin ci gaba da gudanar da wasu muhimman abubuwa da Malaman makaranta suka bukaci yayi masu domin ci gaban fannin Ilmi a fadin karamar hukumar Makoda baki daya.

Daga karshe, Turakin Makoda ya godewa wannan kungiya bisa karamcin da suka yi masa, ya yi mata add`uar Allah Ubangiji Ya karawa kungiyar albarka.

Taron ya samu halartar shugaban kungiyar iyaye na jiha, Dan Hassan da darakta mai kula da shiyya na hukumar kula da manyan makaratun sakarandare na jihar Kano, da tsohon shugaban makarantar sakandare ta gwamnati da ke garin Makoda, Malam Hamisu Rabiu, da darakta a hukumar KEDCO na kananan hukumomin Dambatta da Makoda.

Sauran sun hada da Sakataren ilmi na karamar hukumar Alhsji Nasiru Y. Chidari, da Dagacin garin Makoda, Alhaji Sagiru Adamu Abdullahi da Alhaji Haruna Isyaku Makoda (Garkuwa) da Babban limamin garin Makoda da sauran manya baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: