Kotu Ta Tabbatar Wa Hon. Abubakar Kusada Kujerarsa Ta Majalisar Wakilai
Daga Wakilinmu
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen ‘yan majalisar tarayya a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta soke zaɓen Dalha Ismail Kusada a matsayin ɗan majalisar wakilai.
A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a O. Ogunfowora ta ce Abubakar Yahaya Kusada na APC ne ya lashe zaɓen na watan Fabrairu.
Haka nan, alƙalan sun ayyana Abubakar a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓun Kankia/Ingawa/Kusada.
Kazalika, kotun ta umarci Dalha da hukumar zaɓe ta Inec – waɗanda ake ƙara – su biya Abubakar kuɗi naira 200,000.
Da ma Abubakar ne ke riƙe da kujerar kafin Inec ta sanar da kayen da ya sha jim kaɗan kammala zaɓen, kuma tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina.
Sai dai har yanzu Dalha Kusada na da damar ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.