Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci A Zaɓen Gwamnan Kano


Daga Mujtaba Gali


Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta Jihar Kano ta bayyana Laraba, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan ƙorafi game da zaɓen gwamnan Kano.


Matakin na zuwa ne bayan ƙarar da jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta shigar gaban kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓen jihar, inda take ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan Kano a zaɓen 18 ga watan Maris ɗin 2023.


Shari’ar na cikin manyan ƙararrakin zaɓen gwamna da ke matuƙar jan hankali a Najeriya.


APC ta ce Abba Gida-Gida, bai ci zaɓen gwamnan Kano da halastattun ƙuri’u ba.
Ta kuma ce akwai ƙuri’un da aka soke, waɗanda yawansu ya zarce ratar da ke tsakanin ƙuri’un da Abba Kabir Yusuf da ya samu da mai biye masa wato Nasiru Yusuf Gawuna.


Wani ƙarin ƙorafi da APC ta yi shi ne wanda aka ayyana cewa ya ci zaɓen, babu sunansa a cikin rijistar jam’iyyar NNPP.


Kuma Jam’iyyar NNPP ba ta gudanar da zaɓen fitar da gwani ga masu neman takara, kafin zaɓen gwamnan Kano ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: