Kotu Ta Daure Mutumin Da Aka Kama Da Katin Zabe 101

Daga BBC Hausa

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ce kotun majistare da ke Sokoto ta yanke wa wani mutum mai suna Nasiru Idris da aka kama da tarin katin zaɓe 101 hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta ta Tuwita, ta ce a ‘yan makonnin da suka gabata jami’an ‘yan sanda sun kama mutane a wurare daban-daban a faɗin ƙasar ɗauke da katunan zaɓe masu yawa.

Ta ce a ɗaya daga cikinsu ne ‘yan sanda suka kammala bincike a kansa tare da gurfanar da shi a gaban kotu, inda kuma kotun ta yanke masa wannan hukunci

Haka kuma hukumar ta INEC ta ce nan gaba kaɗan ne za a gurfanar da mutanen da aka kama da tarin katunan zaɓen a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.

A cikin sanarwar hukumar ta ce za ta yi taron wayar da kai da duka kwamishinonin zaɓe na jijohi 36 na fadin ƙasar daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa biyu ga watan Disamba.

A ƙarshen ganawar ne hukumar za ta sanar da ranakun da za ta fara raba katinan zaɓe a faɗin kasar.

Haka kuma hukumar ta yaba wa ‘yan ƙasar bisa hakuri da fahimta da suka nuna, musamman ga waɗande ke buƙatar a sauya musu katunan da waɗanda ke son a sauya musu wurin rajistar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: