Kasuwar ‘Yan Kwallo: Makomar Rashford, Moses, Tielemans, Winks, Dybala, Haaland Da Pogba


Wasan Kwallon Kafa

Arsenal na shirin gabatar da tayin sayen dan wasan Ingila, Marcus Rashford mai shekara 24, ga Manchester United. (Mirror)

Hukumar gasar Premier ta dakile wani yunkuri da kungiyar Burnley ta yi na sayen dan Najeriya Victor Moses, mai shekara 31, daga Spartak Moscow ta Rasha. (Sky Sports)

Dan wasan tsakiya na Leicester City dan Belgium Youri Tielemans, mai shekara 24, ya ce yana son sake wasa a gasar zakarun Turai (Champions League). (Mirror)

Rahotanni na nuna cewa Manchester United da Arsenal na neman sayen Tielemans, wanda Leicester ke son sayarwa a kan fam miliyan 35 a karshen kakar da ake ciki. (Metro)

Southampton da Crystal Palace na sha’awar sayen dan wasan tsakiya dan Ingila Harry Winks, mai shekara 26, daga Tottenham. (Star)

Watakila Paulo Dybala ya bar Juventus ya tafi abokan hamayyarsu na Serie A, Inter Milan, inda Inter ke shirin amfani da dan wasan mai shekara 28 a matsayin wanda zai maye gurbin dan uwansa dan Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 24. (Mail)

Tauraron dan wasan gaba na Borussia Dortmund dan Norway Erling Braut Haaland zai tafi Manchester City ko Real Madrid a bazaran nan, amma kuma dan wasan mai shekara 21 ya yi watsi da babban kwantiragi mai cike da garabasa da City ta gabatar masa. (AS – in Spanish)

Kungiyar Napoli ta yi wa dan wasanta na gaba dan Najeriya Victor Osimhen, wanda kungiyoyi da yawa da suka hada da Arsenal da Liverpool da Manchester United da Newcastle da Tottenham, suka gabatar da bukatarsu ta sayensa, farashin yuro miliyan 100 daidai da fam miliyan 83. (Fichajes – in Spanish)

Paris St-Germain ta sanya ido tare da kasa kunne a kan batun dan wasan gaba na gefe na Leeds United Raphinha, dan Brazil mai shekara 25. (Mail)

PSG ta nuna cewa dan wasan Manchester United, da Faransa Paul Pogba, mai shekara 29, shi ne na farko a wadanda take son saye. (Fabrice Hawkins, via Express)

Haka kuma kungiyar ta gasar Faransa, PSG ka iya neman sayen dan Chelsea Romelu Lukaku, mai shekara 28, a bazaran nan. (Football Insider)

Makomar dan wasan gaba na gefe dan Sifaniya Adama Traore, mai shekara 26, a Barcelona inda yake zaman aro ta dogara ne ga ko Wolves za ta mayar da zaman Francisco Trincao mai shekara 22, da ta aro daga Barcelona ya kasance na dindindin. (Mundo Deportivo)

Haka kuma Wolves din ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiya dan Portugal Ruben Neves a kan sabon kwantiragi, domin dakile sha’awar da wasu kungiyoyi ke nuna wa a kan dan wasan mai shekara 25.(90min)

Inter Milan na fatan cimma sabuwar yarjejeniya da dan bayanta na Slovakia, Milan Skriniar, mai shekara 27. (Gazzetta dello Sport)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: