Kashi 63 Cikin 100 Na ‘Yan Najeriya Na Fama Da Talauci
Daga Mujtaba Gali
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa kashi 63 cikin 100 na ‘yan kasar wato mutum miliyan 133 na cikin talauci.
Alkaluman binciken auna ma’aunin talauci a Najeriya ne suka tabbatar da hakan a yau Alhamis a Abuja.
Hukumar kididdiga ta kasa da hukumar tsara bada tallafi ga masu karamin karfi da shirin samar da ci gaba na majalisar dinkin duniya da asusun ilimin kanana yara na Unicef da shirin yaƙi da talauci da cigaban al’umma na Oxford.
Binciken ya nuna cewa an karɓi bayanan magidanta dubu 56 a sassan jihohin kasar 36 da birnin tarayya Abuja, da aka gudanar tsakanin watan Nuwamban 2021 zuwa Fabarairun 2022.
Bayanan da aka tattara na nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matalauta a kasar na rayuwa ne a yankunan arewacin Najeriya, yayinda kashi 35 cikin 100, kusan mutum miliyan 47 kenan na zama a kudanci.
Sokoto ce jiha mafi talauci a Najeriya, inda kashi 91 cikin 100 na al’ummarta ke rayuwa hannu-baka hannu-ƙwarya, Ondo ce kuma mafi karancin talauci a Najeriya da kashi 27 cikin 100.
A lokacin tsokacinsa a wajen taron bayyana wannan alkaluma, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wadannan alkaluma za su bijiro da hanyoyin fahimtar matsalolin domin yaƙar talauci.