Kasafin kudi na shekarar 2021 zai taimaka wajen aiwatar da tsarin sarrafa kudade na kasa da kasa- Gwamnan Bala

Daga Amina Abdullahi Girbo

Gwamna jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed yace an tsara kasafin kudin jihar na shekara 2021 ne bisa tsare tsaren sarrafa kudade na kasa domin taimakawa wajen aiwatar da tsarin sarrafa kudade na kasa da kasa.

Gwamna bala ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da kasafin kudi ga majalisa dokoki jihar Bauchi na Naira miliyan 213, y ana mai cewa an tsara kasafin kudin ne bisa sarin kashe kudade na matsakaicin zango tare da bada tabbacin cewar gwamnati jiha za ta ci gaba da yin amfani dashi saboda yayi daidai da tanadin dokar kashe kudaden jaha na shekara ta 2009.

Sanata Bala ya kara da cewa an kiyasta kasafin kudin ne bisa hasashen samar da man fetur da farashinsa na kasa da kudin musayar dalar Amurka har ma da kwakkwaran tsarin tara kudaden haraji na cikin gida 

Gwamna Bala Mohd yace a cikin daftarin kasafin kudin gwamnatin sa za ta maida hankali kan aikace-aikace da suke da matukar muhimmanci ga ci gaba jihar.

Yace gwamnatin jiha,a yayi tsara kasafin kudin ta dauki matakai da dama ciki har da manyan aiyukan da za su sabunta birnin Bauchi, aiwatar da manyan aiyukan da suka shafi anobar cutar Covid-19, rage kashe kudade kan aiyukan da ba su zama lalle ba gami da aiwatar da sauran aikace-aikace gwamnati ta dauke su da matukar muhimmanci da kuma ci gaba da kashe kudade kan muhimman aiyukan gwamnati.

Saura sun hada da cimma kasafin kudin da ya dace da yanayin cutar Covid-19, sake farfado da tsarin tara kudaden haraji, rage ma’ aikata na bogi ta hanyar inganta kudin biyan albashi don samun rarar kudade don share hanyar dauka ma’aikata da sauransu.

Ya kuma ce a yayin tsara takardun kasafin kudin,an yi amfani da dabaru na kimiya da tarihi wajen kididdige sha’anin gina tattalin arziki don samar da nagartancen tsarin kasafin kudi na shekara mai zuwa, ya kara da cewa tuni jihar Bauchi ta yi nisa dangane da tsare tsaren sarrafa kudade na kasa.

Gwamnan yace ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na jiha gami da hadin gwiwar ma’aikatu da hukumomin gwamnati da suka dace suna aiki kafada kafada don cimma mataki na kasa da kasa na sarrafa kudade kamar yadda yake cikin tsarin kashe kudade jaha bisa gaskiya da adalci

A game da batun aiwatar da kasafin kudin wannan shekarar 2020,gwamnan yace duk da matsalolin da aka fuskantar daidai gwargwado wajen aiwatar da wannan kasafin kudi.

Da yake maida jawabi,shugaban majalisar dokokin, Abubakar Y Sulaiman ya bada  tabbacin amincewa da daftarin kasafin kudi akan lokaci domin bai wa gwamnati damar aiwatar da aikace aikacen ta da shirye shirye ta kamar yadda suke kunshe cikin tsarin kasafin kudin. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: