Karim Benzema ne gwarzon La Liga na watan Afirilu


Daga Bangaren Wasanni

An bayyana dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema a matakin gwarzon La Liga na watan Afirilu.

Dan wasan tawagar Faransa ya taka rawar gani a wasa shida da ya buga a watan, a fafatawar da ya fuskanci Celta da Getafe da Sevilla da Osasuna da kuma Espanyol.

Real Madrid ce ta lashe dukkan karawar da ta yi a watan da ta kai ta lashe La Liga na bana kuma na 35 jumulla, duk da cewar akwai wasannin da suka rage a kammala kakar nan.

A cikin watan na Afirilu, Benzema ya zura kwallo hudu a raga, inda ya ci Celta biyu da kuma Sevilla da kuma Espanyol da kowacce ya ci guda-guda.

Kawo yanzu Benzema shine ke takarar lashe takalmin zinare a Sifaniya, bayan da ya ci kwallo 26 a raga kawo yanzu shi ne ke kan gaba.
Ranar 28 ga watan Mayu, Real Madrid za ta fafata da Liverpool a wasan karshe a Champions League a Faransa.

Real Madrid ta doke Liverpool 3-1 a kakar 2018 ta lashe gasar Zakarun Turai ta 13 jumulla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: