Karamar Hukumar Hadejia ta Rabawa Matasa Filaye

Daga Aliyu Dangida

Kimanin Matasa 34 ne suka amfana daga rabon filaye wanda Shugaban Karamar Hukumar Hadejia, Alhaji Abdulkadir Bala Umar ya mallaka masu.

A jawabinsa yayin mika takardun mallakar filayen ga matasa, Shugaban Karamar Hukumar yace wannan yana daga cikin kyawawan kudirorinsa wanda ya sa a gaba wajen taymakawa matasa da ababen more rayuwa don su zamo masu dogaro da kansu.

Hon. Bala ya kara da cewa wannan shine somin tabi ne domin akwai daruruwan matasa da za’a tallafawa da kayan aure wasu kayan gini irinsu kwano rufi a gidajensu wasu kuma za’a raba masu jari don su dogara da kansu inda a watanni masu zuwa ake yunkurin kaddamar da tallafin bada jari ga masu kananan sana’o’i kamar yadda aka sanya a cikin Kasafin kudi na shekarar 2021 a karamar hukumar.

A cewarsa filayen da aka rabawa matasan suna kan hanyar Garin Gabas kuma hukumar kula da kasa da safiyo ta Jiha ta buga takardun wanda yanzu haka matasan da suka amfana za su iya ginawa don samun matsugunni na dindindin.

Da suke nuna godiyarsu bisa wannan karamci da Shugaban karamar hukumarsu, Sani Anytime Kakabori Hadejia da Kaninsa, Real Orcarsha da Auwalu Banda sun godewa Hon. Bala Umar tare da yi masa addu’ar fatan alkhairi da Allah Ya biya sa da gidan Aljannah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: