Kane Zai Maye Gurbin Lewandowski, Barca Za Ta Dauki Kounde

Daga BBC Hausa

Babban jami’in Bayern Munich, Oliver Kahn ya kwatanta dan kwallon Tottenham Harry Kane a matakin cikakken mai cin kwallaye,  wanda ke da makoma mai kyau. Ya yabi dan wasan bayan da suka amince za su sayar da Robert Lewandowski ga Barcelona. (Star)

Barcelona mayar da hankali wajen daukar dan wasan Sevilla mai tsaron baya Jules Kounde, wanda ake danganta shi da komawa Chelsea, tuni Barca ta cimma yarjejeniya da Lewandowski. (Marca)

Dan wasan tawagar Netherlands Frenkie de Jong bai son komawa Manchester United ko wata kungiya a Ingila, sai dai dan wasan Barcelona na sha’awar buga Bundesliga tare da Bayern Munich. (Sport – in Spanish)

Bayern Munich ta yi sabon tayin fam miliyan 59.5 da karin fam miliyan 8.5 kudin tsarabe-tsarabe ga dan kwallon Juventus Matthijs de Ligt, inda tattaunawa ta kai matakin karshe. (Goal)

Tottenham na shirin biyan sama da fam miliyan 14 ga Barcelona domin daukar Memphis Depay, sai dai kungiyar Sifaniyna na neman fam miliyan 17, koda yake dan wasan na son barin Camp Nou Camp. (Sport – in Spanish)

West Ham ta taya dan wasan Hertha Berlin, Jordan Torunarigha, wanda Gent, ke son saya, bayan da ya buga mata wasannin aro, sai dai kungiyar Bundesliga na bukatar Yuro miluyan biyar. (Voetbal Nieuws – in Dutch)

Dan wasan Chelsea  Armando Broja zai koma buga wasannin aro a West Ham zuwa karshen kakar bana. Sai dai West Ham na son sayen dan wasan ne, amma dai Chelsea ba ta shirya sayar da dan kwallon ba, wanda ya yi wasannin aro a kakar da ta wuce a  Southampton. (Mail)

Watakila dan kwallon Ingila, Levi Colwill, zai iya barin Chelsea idan kungiyar Stamford Bridge ta dauki masu tsaron baya a bana. (Athletic – subscription required)

Portsmouth, Hibernian da kuma Motherwell na rububin daukat Terell Thomas, bayan Reading ta katse sauran yarjejeniyar da ke tsakaninsu. (Hampshire Live)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: