Kamfanin Apple Zai Fitar Da Sabuwar Wayar Iphone 15


Daga BBC


Nan gaba a yau Talata ne ake sa ran kamfanin Apple zai fitar da sabuwar wayar iPhone ta bana.


Sauran sa’o’i ƙalilan a fitar da wayoyin iPhone 15 da iPhone 15 Plus da iPhone Pro da kuma iPhone 15 Pro Max wato sabbin samfuran a kasuwa.


Duk shekara a watan Satumba ne, Apple yake fitar da sabon samfurin wayar iPhone.
Don haka, tambayar ita ce, mene ne bambancin sabon samfirin iPhone 15 da sauran samfuran wayar iPhone na baya?


Babban bambancin dai shi ne an canza kafa cajin sabuwar wayar zuwa nau’in USB-C, kamar yadda Tarayyar Turai ta ba da umarni a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: