Juventus za ta Dauko Paul Pogba da Di Maria da Kuma Ivan Perisic

Wasan Kwallon Kafa

Juventus za ta karkare a mataki na hudu a gasar Serie A da za a karkare a karshen mako, amma kungiyar ba ta dauki kofi ba a kakar nan.

Hakan ne ya sa kungiyar ke son kara karfin ‘yan wasa don tunkarar kakar badi, bayan da Paulo Dybala da kuma Giorgio Chiellini za su bar Juventus a karshen kakar nan.

Kociyan Juventus, Massimiliano Allegri na sa ran daukar kwararrun ‘yan wasa, don tunkarar kaka ta gaba, wadda ya ke fatan lashe kofuna.

Kwantiragin Paul Pogba zai karkare a Manchester United ranar 30 ga watan Yunin 2022, wanda tuni Juventus ta tuntuba, domin ya sake taka leda a Turin.

Kamar yadda La Gazzetta dello Sport ta wallafa, tuni Juventus ta tattauna da wakilin Pogba, amma ba wata yarjejeniya da aka kulla.

Haka kuma Juventus na sa ido kan dan kwallon Paris St Germain, Angel Di Maria da dan wasan Inter, Ivan Perisic, wadanda kwantiraginsu zai cika a karshen kakar nan.

Di Maria na fatan buga tamaula karin kaka daya a Faransa, idan hakan bai samu ba zai koma taka leda a Argentina.

Dan wasan na fatan buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a bana tsakanin Nuwamba zuwa Disamba, ita ce babbar gasar karshe da zai buga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: