Jigawa 2023 – `Yan Majalissun Tarayya Da Ka Iya Fuskantar Kalubale

              

Daga Aliyu Dangida

Jihar Jigawa na da `yan majalissu 11 da ke wakiltar al`ummomin kananan hukumomi 27 a zauren majalisar tarayya, mafiyawancinsu sun dade a zauren majalisa yayin da wasu basu dadeba, wasu sunyi abin a zo a gani wasu kuwa al`ummomin da suka zabe su suna da nasani.

A yayin da zaben shekarar 2023 ke karatowa masu kada kuri`u sun shiga taitayinsu, inda wasu ke cewa, a zaben shekarar 2015 da na 2019 yawancin zababbun sun shiga rigar alfarma, amma da suka samu nasara sun watsawa masu zaben kasa a ido.

Masu fashin baki naganin cewar zaben 2023 zai sha banban da sauran zabukan musamman idan aka yila`akari da cewar zabukan baya anyi wani abu da ake kira SAK, amma wannan karon SAK ba za tayi tasiri ba. Yayin da wasu ke ganin farin jinin shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa aka zabi mafi yawa daga cikin zababbun wakilai, amma a halin yanzu talakawan kasar sun dawo daga rakiyar tafiyar shugaban kasa da sauran zababbun wakilansu.

Jam`iyyar APC ka iya fuskantar matsaloli a zaben 2023 kamar yadda wasuke hasashen cewar da ma jam`iyyar ta Muhammadu Buhari ce, don haka da zarar yakammala wa`adin mulkinsa APC za ta zama tarihi, al`ummar kasasu za su iya tabbatar da sahihancin wannan magana, musamman idan har sun shiga taitaiyinsu da irin kuncin rayuwa, rashin tsaro, hauhawar farashin kayan abinci, matsalar wuta da tsadar man fetur, da sauran matsaloli da ake zargin jam`iyyar APC ta jefa al`ummarkasa.

Wannan sharhi ko hasashe da muka kawo maku bincike ne aka gudanar tare da ra`ayoyinal`ummar mazabu 11 na `yan majalisar tarayya da ke Jihar Jigawa, wanda suka bukaci a sakaya sunayensu bisa wasu dalilai, amma sun tabbatar mana idan lokaci yayi za su so a wallafa sunayensu inda hali ma har da hotunansu.

A jihar Jigawa kamar yadda mukafada a sama akwai `yan majalissun tarayya da ka iya haduwa da tangarda a takararsu a zaben 2023 idan aka yila`akari da korafin da masu zabe keyi akansu, da kuma mafiyawancisu sun yiwa gwamnati tawayeba a ganinsu a tarukan da gwamnati ke gudanarwa sabanin gwamnatocin da suka gabata, tare da kuma wasu jihohi. ga yadda sharhin ya kasance-

Hon. Ibrahim Kemba Madobi

Hon. Ibrahim Kemba Madobi Dan majalissar tarayya Dutse da Kiyawa– Dan kasuwa kuma dan siyasa, mutum ne mairaha da barkwanci Yakasance a majalisar tarayya tun daga shekarar 2011 a karkashin jam`iyyar APC, yafuskanci babban kalubale a zaben 2019 Allah ne ya taimakeshi yasa munasara. Wata majiya ta tabbatar wawannan kafar yada labarai cewar al`ummar kananan hukumomin Dutse da Kiyawa basu amfana da wani katafaren aikin raya kasa daga wannan wakilinasu, amma da iyakan raba babura, injinan ban ruwa da `yankudade ga masu tsananin rabo. 

Babban kalubalen da Hon Kemba ka iya fuskanta,shi ne, `yan siyasar yankinsa ka iyayi masa tawaye musamman idan aka yila`akari da wasu `yan majalissun jihar da suka jajirce wajen hidimtawa al`ummarsu. Wasu daga cikin al`ummarsa sun yi korafin cewar ganinsa yana yimasu wahala, yayin da wasu kansamu sako ta hanyar wakilansa da ya aminta da su.

Wasu matasa sun yi korafin cewar suna gudanar da sana`arsu, yasa suka sayi fom na aikin soja da zummar zai taimaka masu amma da suka je wajen tantancewa sai koro su aka yi saboda bai nuna a taimaka masu ba. An zargeshi da rashin cika alkawari, yafara wani aiki a rukunin gidajen G9,  wanda yanzu haka yawatsar da aikin, al`amarin da ya jefa al`ummar wajen cikin wani hali musamman ga damuna nazuwa.

Rahoto daga majiya maikarfi a zauren majalissatarayya ta tabbatarwa Mahangar Arewa cewa, a kwanakin baya an haramtawa Hon, Kemba zaman majalisar bisa wani babban abin kunya daa kezargin ya tafka, wanda haka ana ganin ka iyakawo masa cikas a neman sake tsayawa takararsaa zaben 2023.

Akwai `yan siyasa wadanda suka jajirce wajen hidimtawa al`umma a matakin jiha da matasa masu jini a jika da suka fito tare da nuna sha`awarsu na yin takarar majalisar tarayya Dutse da Kiyawa wadanda kuma ake tunanin za su zame masa babban kalubalena rasa kujerarsa a 2023.

Wasu naganin halin rashin lafiya da ke damun Hon. Kemba wadda ana tunanin yadade a kasar waje don neman magani ka iya sa yayi asaran da takararsa. Yayin da wasu daga cikin hadimansa naganin gwanin nasu zai kai labari a zaben 2023, musamman idan aka yi la`akari da irin ayyukan da yasamarwa al`ummar kananan hukumomin Dutse da Kiyawa.

Hon. Magaji Da`u Aliyu

Hon. Magaji Da`u Aliyu Dan majalissar tarayya Birnin-Kudu da Buji– Jajirtaccen dan siyasa kuma kwararren injiniya wanda baya da na biyu wajen hidimtawa alummarsa tunda aka zabenshi a shekarar 2015, yakasance a koda yaushe yana gudanar da taron bada tallafi ga al`ummarsa da ke wadannan kananan hukumomi biyu (Birni-Kudu/Buji), yakawo ayyukan da dama a fadin yankin da yake wakilta, kuma al`ummarsana tare da shi, sai dai akwai kalubalen a gabansa a zaben 2023 duk da wadannan ci gaba da aka lissafo a sama.

Babban kalubalen da zaisamu, shi ne, tun da aka fara mulkin dimokuradiyya a shekara 1999, karamar hukumar Buji bata taba samun dan asalin yankin yazama dan majalisar tarayyaba, don haka a wannan karon mutane yankin sun fito ka`in da na`insai sun tabbatar da an zabi dan su a zaben 2023 don ya wakilcesu.

Wannan ne yayi sanadin wani dan karamin tashin hankali a yayin wata ziyarar bada tallafi da ya kai karamar hukumar Bujiin da aka jikkatawasu magoyabayansa tare da lalata motocin da ketawagarsa. Wasu daga cikin jiga-jigan siyasar karamar hukumar Buji sune matsalarsa, anzargeshi da girman kai da wulakanta mutane wanda ka iya zame masa babban kalubale a zaben 2023 in har hakan gaskiya ne.

Akwai wani jigo a gwamnatin jihar Jigawa wanda ya tsaya takara a wancan karon amma bai samu nasaraba aka ce yahakura don haka a zaben 2023 za a yi fito na fito ne don gwada kwanji tsakaninsa da Hon. Da`u.

Hon. Yusuf Shittu Galambi

Hon. Yusuf Shittu Galambi Dan majalissar tarayyaGwaram– Dan siyasa daga tushe yana tare da mutanensa kuma yana hidimtamasu, yakasance jigo a siyasar Gwaram da kewayenta, mazabarsa nadaya daga cikin mazabu mai yawan al`umma a jihar Jigawa. Yataba zama zababben dan majalisartarayya a karkashin jam`iyar PDP, yane mitakarar kujerar Sanata inda bai samu nasaraba a zaben 2019.

A wancan lokacin yana dagacikin `yan majalissu da al`ummar Jigawa ke alfahari da shi domin kuwa yakasance na farko da yafara budeo fis a shiyyarsa, kuma ya samarwa mutane ayyuka da dama tare da kawo tashar talabijin ta kasa NTA a karamar hukumar Gwaram da sauran ayyukan rayakasa.

Bincike ya nuna cewar a wannan karon dan majalisa Galambi yacanja halayensa domin kuwa yasamu nasarar komawa majalisar tarayya sakamakon rasuwar dan majalissar yanki, Hon Yuguda Kila.

Inda sai da aka kai rwa  rana sannan yasa mutsallakewa, yayin da aka samu rarrabuwar kai tsakanin gwamnati, wasu jigogin jam`iyyar APC suna ganin cancanta yayi a bai wadan marigayin kujerar mahaifinsa, wane tudu wane gangare Allah Yakadar ta Galambi yasamu nasara.

A wannan karon Galambi yana fuskantar matsaloli daga bangarori biyu zuwa uku, daya gwamnati wadda yake gani ta taka rawa wajen dakile takararsa, a hannun daya kuma magoya bayan marigayi tsohon dan majalisa wanda suke ganin Galambin ya share su baya tafiya da su a harkokin mulki duk da gudunmawar da suka bashi a zaben.

Gwamnatin naganin Galambi yazama kanwa uwar gami tsakanin al`ummar Gwaram inda ko a watannin baya wani daga cikin magoya bayan saya rasa mukaminsa a gwamnatin jiha sakamakon zargin da ake nasa hannun Galambi wajen hada wata zanga-zanga a gidan gwamnati.

Wadannan da wasu halin ko in kula da yake nunawa wasu daga cikin al`ummar da suka zabeshi sabanin wancan lokacin da yakasance a matsayin wakilinsu ka iya zame masa cikas din takararsa. 

Hon. Sa`idu Yusuf Miga

Hon. Sa`idu Yusuf Miga Dan majalissar tarayya Jahun da Miga– Gogaggen dan siyasa kuma tsohon malamin makaranta kafin yatsunduma harkokin siyasa, wanda yarike mukamai da dama kafin samun damar zama wakilin al`ummar Jahun da Miga a shekarar 2003 zuwa 2011, ana masa lakabi da Bango.

Yakara samun nasarar zama dan majalisar tarayya a karo na biyu a zaben 2015, al`umma musamman na karamar hukumar Jahun na da korafi akansa nahalin ko in kula da rashin tabuka abin azo a gani, wannan shine babban kalubalen da zai fuskanta a zaben 2023.

Al`ummarsa nakorafin rashin zuwansa kuma basu da inda za su same shi don gabatar masa da matsalarsu, babu ayyukan ci gaba ko daukar matasa aiki da yayi a wannan karon kamar yadda suke korafi. Sun fadawa kafar wannan sadarwa cewar rabon da su sashi a idanunsu sun fi shekara biyu ko taron gwamnati baya zuwa bare ta`aziyya ko jaje, wasu na cewa yakanyi baddabami da daddare ya kai wa wasu daga cikin al`ummarsa ziyara.

Hon. Miga yana fama da kalubale daga manyan `yan siyasa na karamar hukumar Jahun wanda suke gani su yakamata ace sun taka wannan matsayi ganin suna da gogaggun `yanboko, wayayyu da sanin makamar aiki fiye da Miga.

Hon. Ado Sani Kiri

Hon. Ado Sani Kiri Dan majalissar tarayya Ringim da Taura– Tsohon shugaban karamar hukumar Taura, tsohon kwamishina a ma`aikatun da dama, tsohons hugaban jam`iyyar APC na jihar Jigawa kafin zabensa a matsayin wakilin al`ummar Ringim da Taura a majalisar kasa.

Yakasance mutum mairaha da jajircewa wajen kyautatawa al`ummarsa musamman lokacin da yake rike da wadannan mukamai da aka lissafo a sama. Ana masa lakabi da Gwanki.

Al`ummar da suka zabi Ado Sani a matsayin wakilinsu sun koka ainu da cewar ya canza domin kuwa ba Adon da sukasani bane, sun ce ba a samunsa  awaya ko an same shi ma bazai daukaba, sannan bazai biyo kiran daga baya ba.

A shekarun farko da na biyu a majalisa bayan zabensa, al`umarsa sun yiittifaki ban da dumama kujera da rashin kawo ci gaba a yankin ba wani abin da za aiya alfahari da shi.

A cikin shekara ta uku sun ce yadan tabuka abin azo a gani, inda ya tallafawa wasu daga cikin mutane kananan hukumomisa, amma duk da haka sun nuna rashin gamsuwa da wakilcinsa inda suke jiransa ko zai sake nuna sha`awar tsayawa a 2023, anan fa  zasu nuna masa shayi ruwa ne, domin sun ce an sha su sun warke.

Idan muka koma sauran kalubale da Kiri ka iyafuskanta shine a matsayinsa na gogaggen dan siyasa yayi wasa da dammarsa domin kuwa ya biyewa wasu daga cikin abokansa wajen yin`yan sharholiya inda shi ma yakasance cikin daya daga cikin `yan majalissun da sukakunyatajiharsu da al`ummarsu a zaurenmajalisaharyahaifar da dakatar da shi daga zuwa zaman majalisa na tsawon wani lokaci.

A matsayinsa na tsohon shugaban jam`iyar APC na jihar Jigawa ya shiga sahun `yan majissun da sukayi wa gwamnati tawaye, bai cika halartar taron da gwamnati ke kira ba, an fi ganinsa  ataron da shugaban kasa ke zuwa jiharsa. Zuwansa majalisa yas al`umma da damasu ke ganin ba Adon da sukasaniba ne, saboda ya canza halaye da mu`amalarsa.

An ruwaito cewar Hon. Kiri ya tabbatar da cewar zai samu matsala a zaben 2023 don haka yawatsar da mutanensa ya tuba da kyautata masu, wata majiya ta tabbatar da cewar Hon. Kiri yasanar da cewar bazaiyi takarar a zaben 2023 ba, a cewarsu wai irin abubuwan da idanunsa su ka gane masa a shekara 4 da yayi a zauren majalisa bazai iya jurewa idanunsa su sake ganiba don haka yahakura da takara inda yacea kai kasuwa.

Akwai masu neman kujerarsa ko a mutu ko ayi rai, wasu kuma gwamnatice za ta tsayar da su saboda mukamin iyayensu duk da basu cancanta a matsayin ba, fatan dai kada al`ummar Ringim da Taura suce gara jiya da yau a wakilicin majalisar tarayya.

Hon. Musa Muhammad Fagen Gawo

Hon. Musa Muhammad Fagen Gawo Dan majalissar tarayya Babura da Garki-Yaro ne matashi da yasamu dama amma bai yi amfani da damarsaba, Yakasance zababben wakilin al`ummar Babura da Garki sakamakon mutuwar mahaifinsa ta hanyar amfani da karfin gwamnati.

Akwai goggagun `yan siyasa da suka fito daga yanki masu ilmi da sanin makamar aiki amma gwamnati ta dage sai dan marigayin ya maye gurbin kujerar mahaifinsa bias wani dalili da itagwamnati ta sani, amma wasu na cewar marigayi Fagen Gawo wai yadauki zubin adashe wanda ake so shi yaron ya ci gaba da yiwa mahaifinsa zubi a matsayin hanya da za a warware wannan bashin.

Wakilcin Matashi Fagen Gawo bai amfanar da al`umomin Babura da Garki da komaiba, domin kuwa bawani aiki guda daya da yakawo na ci gaban yan kunan, hasalima ya biyewa abokan sharholiyaa Abuja suna ta cin karensu ba babbaka yakyale wadanda suka zabeshi da zarei danu.

Wasu naganin abin daya takureshi har yagaza tabuka komai shine rashin gogewa da samun dama a bagas ba tare da sanin darajar kujerar ba, wasuna da ra`ayin dama ai yasanan zabe shi don yabiyawa mahaifinsa bashi don haka ba aiki kula al`ummake gabansaba.

Bincike na nuni da cewa akwai manyan kuraye a gabansa wadanda suke ganin za su iya ficewa daga jam`iyyar APC idan aka hanasu takara, bisala`akari da sun fi shi zama cancanta akan kujerar.

Hon. Nazifi Muhammad Fulawa

Hon. Nazifi Muhammad Fulawa Dan majalissar tarayya Gumel, Sule-tankarkar, Gagarawa da Maigatari-

Yana daga cikin matasan `yansiyasa da suka samun nasarar shiga cikin guguwar sauyi ta jam`iyyar APC n Buhari a zaben 2019.

Ya samu dama kuma yayi abinda zaiyi al`ummarsa, a matsayinsa na sabon yankan rake wanda baya da gogewa a harkar siyasa bai biye wa sauran matasa wadanda suka samu dama irin ta saba ammasu ka watsar da mutanen da suka zabesu.

Ko bakomai al`ummar kananan hukumomin 4 da yake wakilta sun dandana romon dimukuradiyya a lokacin wakilcinsa sabanin wakilcin baya na wanda yakarba daga gareshi, Nazifi yagabatar da ayyukan rayakasa da bada tallafi tare da samarwa dimbin matasa ayyukan yi.

Babban kalubalen da ka iyazame masa cikas a takararsa a zaben 2023 shine akwai gogaggun `yansiyasa da suke sunsunar kujerarsa wadanda gwamnati ke da ra`ayi akansu maye gurbinsa. Wasu  daga ciki sun dandana dadin ta wasu kuma sunajin labari, rashin kawo ziyara akai-akai zuwa mazabunsa da mahaifarsa na daga cikin abinda aka lissafo ka iya kawo masa cikas. 

Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Hon. Muhammad Gudaji Kazaure Dan majalissar tarayya Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi– Suna masa lakabi da cali-calin majalisa ko dan majalissar barkwanci, shi kuma yana kirankansa da “Speaker of the Masses” yayin da wasuke ganin ai kunyata al`ummar mazabunsa yake wajen tashi ya rinka harbatamati a zauren majalissa musamman masu ilmina Kazaure. Ko bakomai sun ce yafi wakilcin baya domin ana ganinshi yana tashi tare da kawo kuduri.

Yakasance matsahin dan siyasa maikarancin shekaru da ilmi a tarihin zauren majalisar tarayya wanda shi ma alfarmar guguwar APC ta shekarar 2015 yashiga, an sha fama da cece-kuce akankomarwa majalisar a zaben 2019 amma yashiga yafita haryasamu komawa a karo nabiyu.

Masu fashin baki a yankin sun ce tun bayan komawarsa a karo nabiyu aka daina jinduriyarsa, yadaina zuwa gaisuwar mutuwa, daurin aure, jaje da sauran abubuwa da su kashafi mutanensa, said ai wakilci. Sun tabbatarwa da wannan kafarsadarwa cewar ko a Kano inda yake zaune da iyalinsa ka kai masa ziyara zaice ai kudinsa sukasa yaci zabe don haka baruwansa da kowa.

Duk da wannan matsalar bata hanashi samarwa daidaikun mutane aikiba musamman wanda sukeyi  masa biyayya, domin shine shugaban wanda idan aka kalubalanceshi a kafafensa da zumunta na zamani zai maida martani da kansafiye da yadda aka yi masa, abinda mutane ke ganin ba girman kujerarsaba ne, kuma bai cika faruwa dan majalisa yarinka sainsa da mutanensa sai dai magoya bayansa surama masa.

Halin ko in kula da yake nunawa al`ummarsa gami da daukar bangare nacewar idan bakayi da shi, shi ma baya yi da kai, rashin muhallinakansa a mahaifarsa da tabargaza da wasuke ganin yanayi gami da zargi wasu daga cikin mugayen dabi`unsa ka iyazame masa babban kalubalena sake samun nasara.

Al`ummarsa na korafin cewar yana nuna banbanci  atsakaninsu inda yakarkata hankalinsa wajen wadanda suke masa biyayya, yayinda wadanda suke ja-in-ja da shi yafitaharkarsu. Hon. Gudaji ka iyacin alfarmar da wasu gwamnonisu kanema masa a wajen gwamna Badaru don samun nasarar cin zaben 2023 musamman idan har Gwamnan ya manta da irin sainsa da sukayi a shekarar da ta gabata wadda sai da aka shiga tsakaninsu.

Hon. Abubakar Hassan Fulata

Hon. Abubakar Hassan Fulata Dan majalissar tarayya Guri, Birniwa da Kirikasamma

Dan siyasa ne da ke tare da mutanensa kuma yana hidimta masu a kowane lokaci, masu fashin baki na yankin sun ce mutum ne mai karrama dan adam ko da bazai zo da kansaba, yakan aiko da sako idan wani abu yasamu daya daga cikin al`ummar da yake wakilta.

Dan siyasa ne kuma maiilmi, ya aiwatar da ayyukan rayakasa masu nasaba da inganta rayuwar al`ummarsa wanda suka hada da gina tare da gyaran makarantu da asibitoci, samar da ruwan sha, raba ababen hawa ga shugabannin jam`iyya da mazabu, gina hanyoyi da sauransu.

Anyi ittifakin cewar aikin zababbun wakilan dake majalisartarayya dake wakiltar masarautar Hadeja badan siyasar da yake da kyakkyawan mu`amala da mutanensa irin Abubakar Fulata ya kan zagaya kananan hukumomi uku da yake wakilta ba tare da shakku ko tsoroba, sabanin wasu wakilai da ba za suiya kai ziyarar ta`aziyya, suna, daurin aure ko makamanciyar haka ba saboda rashin cika alkawari da sukayiwa al`umma.

Matsalar da ka iyakawo masa cikas amma balalle ta yi tasiriba, itace wasu daga cikin jami`an gwamnati da ke ganin lokacinsu ne su wakilci wannan mazabu guda uku, ganin cewar DoktaFulata yafito daga karamar hukumar Guri kuma sun dade suna wakiltar sauran al`umma don haka akwai `yansiyasa daga kananan hukumomin Birniwa da Kirikisamman da mutanen yankunan ke ta kiraye-kiraye don sufito takara a 2023.

Hon. Fulata ya samu hallaci da tago mashi daga wajen al`ummar da yake wakilta na kananan hukumomi 3 inda suka hada masa kudin sayen fom din tsayawa Takara a zaben 2023 a matsayin wakilinsu a karo na uku a bias dalilin da suka bayyana cewar tunda aka dawo mulkin dimukuradiyya a shekarar 1999 basu taba samun wakili kamar Hon. Fulata ba.

Hon. Ibrahim Usman Kamfani

Hon. Ibrahim Usman Kamfani Dan majalissar tarayya Hadejia da Auyo-

Dan siyasa daya tilo da yayi fice a cikin sauran `yan siyasar jihar Jigawa, yana gudanar da ayyukan raya kasa da tallafawa al`ummarsa amma ba a tabagani ko ji a wata kafar sadarwa ta zamani, radiyo ko jaridu yana tallata ayyuukansa ko kuma tallafi da ya bai wa al`ummar da suka zabeshi a bainar jama` a ba.

Magoya bayansa sun ce idan Kamfani zai yi maka alheri ba wanda zai sani, idan zai bada tallafi sai dai yakira shugabannin mazabu yadan kamasu su je su bai wawanda ake so a basu. “Samun wakilci irin na Kamfanisai an bincika, don kuwa yana kyauta ko gabatar da ayyukansa saboda Allah bafariya, ba gori ko hantara, sabanin wasu `yan siyasa masuyiba don Allah ba, daga baya har surinka yiwa mutane gori”. In ji wani dan siyasa a yanki da yace a sakaya sunansa.

Wadannan halaye na karamci da yakana idansu za abi babu tantama samun wanda zai kara da shi a zaben 2023 harya kai ga nasara zai yi wuya, musamman idan aka yi la`akari cikin garin Hadejia suna da Sanata. Sai dai masu fashin baki naganin wasan ka iya canjawa idan lamba biyuna jiha bai samu takarar gwamna ko sanataba mai yuwa idan yanunasha`awar wakilcin  majalisar tarayya ayi karfa-karfa.

Amma masana siyasa a yankin sun yi ammana cewar babu wani dan siyasa da zai iyafafatawa da shi har ya kai ga nasara a wannan yanayi da ake ciki, wannan al`amari kuwa,  al`ummar yankin za su yanke hukunci waya kamata suzaba a 2023 a matsayin wakilinsu.

Hon. Abubakar Makki Yanleman

Hon. Abubakar Makki Yanleman Dan majalissar tarayya Kaugama da Malam Madori-

Yana daga cikin `yansiyasa kuma wanda suka bada gudunmawa fiye da gwamnatin jiha a yan kunan da yake wakilta a majalisartarayya, shine dan majalisar da yayi taron tallafawa al`ummarsa da yagigita sauran takwarorinsa `yanmajalissu, gwamnati da jami`anta wanda sukarinka tambaya ina yasamo kudin da yasayi kayan tallafinnan?.

Ya samawa matasa ayyukanyi a hukumomin gwamnatin tarayya tare da daukar nauyin karatun daruruwan matasa a makarantun gaba da sakadaare dake fadin kasar nan, mutanensa sun yaba da wakilcinsa, amma ba a nan gizon yake sakaba, ana tunanin gwamnati ta shigo da wani ra`ayinta a zaben 2023 wanda ka iyazame masa targanda ko sanadin rasa kujerar, wandashirye-shirye sun yinisa na takarar wata jigo kuma `yar gidan sarautar daya daga cikin kananan hukumomin da yake wakilta dadindadawa tana daga cikinmasu fada a ji a gwamnatin da maigidan takejagoranta.

Wannan sharhi ko hasashe da mukakawo maku bincike ne aka gudanar tare da ra`ayoyinal`ummar a mazabu 11 na `yan majalisar tarayya da ke jihar Jigawa wanda suka bukaci a sakaya sunayensu bias wasu dalilai, amma sun tabbatar mana idan lokaci yayi za su so a wallafa sunayensu inda hali ma har da hotunansu.

Dadin dadawa an gudanar da shi bada niyyar cinmutunci ko tozartawani daga cikin `yan majalissun 11 najihar Jigawa, sai dai an yi ne don abinda Bahaushe kecewa “Gyara Kayan ka baya zama sauke mu raba”, fatan mu shine Allah Ya bai wa mairabo sa`a, kuma masu zabe suyi karatun ta nutsu wajen zabe kada san rai ya kai su ga nadama domin bahaushe nacewa “Da sabon gini gwara yabe”.

Don haka lokaci da al`ummar da ake wakiltasu za suyialkalanci tare da zaben wanda suka ga ya dace ya sake mulkarsu, domin kuwa sun cewai an yiwalkiya… don haka kan mage yawaye ba za sukara yadda a sha su basilla ba.

Zaben 2023 dai zai kasance al`umma za suyi duba natsanaki ba tare da bin ra`ayinwasu ko kuma kudi suyi tasiriba domin kuwa bahaushe nacewa Jiki Magayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: