Jamiyyun APC Da PDP A Zamfara Sun Kalubalanci Faifan Audio Da Anas Anka Ya Yada

Daga Hussaini Ibrahim

Mukaddashin Shugaban jam’iyyar PDP, Muktar Lugga,ya yi zargin cewa, a wani faifan Audio da aka yada, mai dauke da muryar Anas Anka, manajan daraktan gidan talabijin na Thunder Blowers,na yanar gizo, ya fito karara ya yi alfahari da yadda tsohon Gwamna Abdulaziz Yari ya bashi kudade don bada cin hanci a shari’ar da ake yi yanzu haka ta zaben da ya gabata.

Lugga ya yi ikirarin cewa, an ruwaito tsohon gwamnan ya bayar da cin hanci ga ‘yan majalisar dokokin jihar don fara shirin tsige Gwamna Dauda Lawal.

Hakazalika, faifan sautin ya nuna cewa Anas Anka na yin zarga -zirga bangaren shari’a, musamman alkalan kotun sauraron kararrakin zabe na jihar wadanda ya ce an sa su gabatar da hukunci ga APC.

Ya ce “Mun umurci lauyoyin mu da su gaggauta shigar da kara da fatan hukumar shari’a za ta yi amfani da damar wajen gyara duk wani rashin adalci da ba a gane ba”.

Lugga, yayi kira ga majalisar shari’a ta kasa, NJC da ta bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa alkalan kotun.

Mukaddashin shugaban PDP na jihar ya kuma yi kira ga hukumar DSS da ta gayyaci Manajan Daraktan Thunder Blowers ta yanar gizo domin yi masa tambayoyi akan shari’o’in gwamnoni da na majalisar dokokin jihar da ba’a bayyana ba hukuncin ba a yanzu a Kotun Koli.

A nata bangaren jam’iyyar APC, Sakataren yada labarai na Jamiyyar ,Yusif Idris, Gusau ya bayyana cewa, ta musanta faifan sautin da Sanata Abdulaziz Yari da Anas ya yi ikirarin cewa ya karbi kudi daga hannunsa.

“Lokacin da INEC ta yanke shawarar bai wa PDP kujerar gwamna bayan kammala zabe da kuma lokacin da kotun ta bai wa PDP majalisar dokokin jihar Maradun ll, ba mu yi ihun rashin adalci ba don kawo cikas ga shari’ar kotun don haka PDP dole ne a sani cewa ba za a iya tsoratar da bangaren shari’a na Nijeriya da irin wannan zarge-zargen marasa kan gado da PDP ta yi ta hanyar Anas ba”.

Jam’iyyar APC ta bukaci dukkanin jami’an tsaron da abin ya shafa a kasar nan da su bankado duk wadanda suka aikata wannan aika-aika ciki har da wanda ya yi wannan faifan tunda duk tare da hukunta su.

“PDP ta fahimci cewa bangaren shari’a hukuma ce mai zaman kanta, kuma babu wani abin tsoro ko cin zarafi da zai hana ta yin adalci ga dukkan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko siyasa ba.

“Jam’iyyar ta kuma yi kira ga magoya bayan jihar da su kwantar da hankulan su domin muna da yakinin za a yi mana adalci kuma za a kwato mana hakkinmu da aka sace wanda ‘yan bangar da wasu sojoji marasa kishin kasa suka yi a lokacin zabe.

“Kuma kowa ya san Anas Anka ,dan PDP ne dan Dauda Lawal ya bashi Ofishin da ya kafa kamfanin sa.harda mota”.in ji Yusif Idris Gusau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: