Jam’iyyar Labour Da Peter Obi Sun Kasa Ci Gaba Da Gabatar Da Bayanai A Kotu


Daga BBC


Jam’iyyar hamayya ta Labour a Najeriya da dantakararta Peter Obi sun kasa ci gaba da bayar da bahasi a karar da suka shigar a gaban kotun zaben shugaban kasa, a yau Laraba.


Kotun ta ba su karfe 9 na safe a yau Laraba, domin ci gaba da gabatar da bayanansu a gabanta ta hanyar kawo karin shedu da takardu, inda aka ba su sa’a hudusu yi hakan.


Sai dai yayin da kotun ta zauna, lauyan masu karar, Awa Kalu (SAN) ya gaya wa alkali cewa sun shirya gabatar da wasu takardu, amma kuma suka gamu da wasu matsaloli daga sakatariyarsu inda wasu ma’aikatansu biyu da za su hada takardun ba su da lafiya.


A kan haka ne ya nemi kotun ta daga musu kafa zuwa gobe Alhamis.


Lauyan hukumar zabe Abubakar Mahmoud (SAN) da, Wole Olanipekun (SAN) na Bola Tinubu da Kashim Shettma, da kuma Lateef Fagbemi (SAN) na jam’iyyar APC ba su kalubalanci bukatar ba.


Sai dai lauyan INEC din, wato Abubakar Mahmoud ya bukaci kotu ta zafatare yawan kwanakin da ta ba su na gabatar da bayanansu saboda wannan matsala da suka zo da ita.


A karshe dai babban alkalin kotun, Justice Haruna Tsammani ya amince da bukatar lauyan na Labour da Peter Obi, inda ya daga musu kafa har zuwa gobe Alhamis da karfe 9 na safe.


Kotun ta dage zamanta zuwa karfe 2 na rana a yau din lokacin da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da dan takararta Atiku Abubakar za su ci gaba da gabatar da bayanansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: