Jami’an tsaro sun koma Garin Shinfida domin tsare rayukan al’ummar

Daga Muhammad Aminu Kabir

Wasu Labarai da suke fitowa daga ƙaramar hukumar Jibia sun bayyana cewa an maida Jami’an tsaro da aka ƙwashe a baya domin bada tsaro ga al’ummar garin.


Idan dai ba’a manta ba a wasu mazauna garin sun bayyana cewa, da safiyar ranar Alhamis 10 ga watan Maris, 2022, wasu motocin Jami’an tsaro, suka shiga garin suka ƙwashe jami’an tsaron garin ba tare da bada wata sanarwa ba dalilin da yasa su ma mutanen gari su kayi ta kansu, wanda a lokacin sakamakon turmutsutsu har aka rasa rayukan mutane sama da Bakwai.


Al’ummar ƙauyen Shinfiɗa na cikin mawuyacin hali sakamakon rashin jami’an tsaron da za su basu kariya kasancewar ‘yan ta’adar daji na yawan kawoma garin hari, kuma zaman Jami’an tsaron a cikin garin ne ya hana barayin daji shigo garin saboda su ma suna tsoron abinda zai iya faruwa da su.


Yanzu dai jama’a sun fara murna tare da shirin komawa gidajen su domin ci gaba da rayuwa, ba da jimawa ba Shugaban ƙaramar Hukumar ta Jibia ya kai ziyarar gani da ido a garin na Shinfiɗa inda ya gane ma idon shi abinda ya faru yayi kuma alƙawalin ƙoƙarin gina ma garin hanya wadda tsawon ta zai kai kimanin kilomita goma.


A baya dai garin na Shinfiɗa sai da ya zama kufai ko dabba babu balle Ɗan adam sakamakon aikin ‘yan ta’adar daji da ya addabi garin.


Ko a baya dai ‘yan bindigar sun aike da saƙonnin barazana ga mutanen ƙauyen cewa madamar dai babu Jami’an tsaro a garin toh tabbas za su zo su afkama garin.


Jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarin su wajen bai wa jama’a kariya sai dai su ma suna fuskantar barazana daga hare-haren ‘yan ta’adar, munaaddu’ar Allah ya ba su kariya ya zaunar damu lafiya Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: