Inganta Noma Ta Hanyar Zamani Da Yakar Talauci Ga Yan Kasa Na Daga Manufar Shugaban Kasa Mai Jiran Gado – Amb Rabi Dangizo

Daga Rabiu Sanusi Kano

Shugabar kungiyar PAPSA ta kasa Hajiya Rabi Garba Dangizo ta bayyana batun noma ta hanyar zamani na daga cikin manufar shugaban kasa mai jiran gado a najeriya a nan da dan lokaci.

Rabi Dangizo tace Tinubu ya yi maganar samar da Ingantattun hanyoyin inganta harkokin noma a kasar nan musamman Samar da kayan na zamani da taimakama manoman da dukkan tallafin da ya dace.

“Idan aka koma wajen batun fitar da kayan manoma kuma a kasar nan yana da niyyar taimaka ma manoma bangaren fitar da kayan gonar su zuwa kasashen ketare.”

DG PAPSA ta ce kuma wajen harkar sufuri akwai shirin samar da dukkan kayan da suka dace kama daga tituna da hanyoyin jirgin sama da sauran su musamman a arewacin kasar nan dan rage matsalolin da suke ciki.

Kazalika tace batun tsaro kuwa Tinubu zai samar da dukkan mai yuwuwa ganin ya kawo karshen matsalar tsaro dake addabar kasar nan.

Wajen maganar rage rashi aikin yi kuwa da rage zaman banza, shugaban kasar na da kudurin kawo hanyoyin samar da dukkan hanyar dogaro dakai.

DGn ta tabbatar da tsari mai kyau da zababben shugaban kasar zai yi amfani dashi wajen sauya akalar najeriyar ta hanyar cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: