INEC Ta Dakata Da Aikin Rajistar Zabe
Daga BBC Hausa
Hukumar zaɓe a Najeriya ta ce dokokin Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ba su ba ta damar ta ci gaba da yin aikin rajistar kaɗa ƙuri’a ba kafin babban zaɓe na 2023.
A ranar Talata ne rahotanni suka ambato Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci hukumar ta ci gaba da aikin rajistar har zuwa saura kwana 90 kafin zaɓen.
Independent National Electoral Commission (INEC) ta rufe aikin rajistar zaɓen a watan Yuli da ya gabata, abin da ya jawo martani da koke-koke daga ƙungiyoyin farar hula cewa za a tauye wa miliyoyin ‘yan ƙasa haƙƙinsu.
Amma da yake magana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a ranar Talata, Kwamashinan Wayar da Kan Masu Zaɓe na INEC Festus Okoye ya ce hukumar ba ta samu kwafin hukuncin ba tukunna.
Ya ƙara da cewa: “Abu ne da ba zai yiwu ba a tsarin Kundin Tsarin Mulki ga INEC ta ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe.”
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, saura kwana 93 da awa 7 a fara kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen da za a gudanar a watan Fabarairu, inda ‘yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da na jiha.