Ilimin addinin musulunci shine kashin bayan zaman lafiyar kowacce al’umma… Masari

Daga Wakilinmu

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana ilimi musamman na addinin musulunci a matsayin wani kashin bayan zaman lafiyar kowacce al`umma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin bikin taron bude Islamiyya da Masallaci wanda Gidauniyar Su’Ad Al’Abdul Jaleel da ke kasar Kuwait ta gina wa al’ummar Kafur, Masari da kewaye.

Gwamnan, wanda ya dauki lokaci yana jaddada muhimmancin neman Ilimi da kuma taimakawa addinin Allah, ya ja hankalin jama’a da kada a raina girman aikin da za ayi ko karancin dukiyar da za a zuba wajen daukaka da kuma yada kalmar Allah.

Gwamnan ya kara da cewa, hatta rashin imani da rashin tausayin da ‘yan ta’adda suke yi mafi rinjaye jahilci ne da kuma rashin sanin addini.

A karshe, bayan godiya ga dukkanin wadanda suka bada gudunmawa wajen wannan aiki, Aminu Bello Masari ya umurci Dangaladiman Katsina Hakimin Kafur Alhaji AbdurRahman Rabe Abdullahi da ya tabbatar da an kafa kwamiti mai karfi wanda zai rika kula da wannan domin al’umma su sami ci moriyar wurin yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: