Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas Ta Bada Gudumawar Kayakin Abinci

Daga Amina Abdullahi Girbo

Hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ta bada gudumawar kayakin Abinci da wadanda bana Abinci ba ga mutanen da Anbaliyar Ruwan ta shafa a kauyuka daban daban na Wannan jaha Shugaban Hukumar, Muhammad Goni Alkali a yayin da bada kayakin ga jaha, ya kara bada tabbacin kudurin Hukumar na Samar da tallafi ga mutanen da annoba ta shafa a Wannan yanki.

Ya bayyana cewar kayakin sun hada ne da buhunan shinkafa masu nauyin kilogram 25 guda dubu goma, galan dubu 3 na man Girki, barguna dubu biyar, Tabarmai dubu biyar, Turamen zannuwa dubu biyar da kayan sawa na yara dubu 3.

Yace a lokacin da akayi bikin ranar jin kan bil Adama ta duniya a garin Maiduguri a kwanaki baya Hukumar tayi Alkawari tallafawa jihohi 6 na Wannan yanki da kayakin Tallafi ta hannun kwamitin shugaban kasa kan sake tsugunar da yan gudun hijira.

Da yake maida jawabi, Gwamna Bala Abdulkadir Mohd ya yabawa Hukumar bisa bada wannan gudumawar, yana mai bayyana gudumawar da cewa ta zo akan gaba tare da bada tabbacin nuna adalci wajen rabar da kayakin ga wadanda abin ya shafa.

Sai ya yabawa wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa taimakawa Hukumar da yake yi domin Bayar da tallafi ga mutanen da annoba ta shafa su a Wannan yanki na Arewa maso Gabas yana mai nuni da cewa, taimako daban daban da Hukumar ke bayarwa zai taimaka wajen shawo kan matsaloli daban daban da Wannan yanki ke fama dasu.

A cewar Gwamnan kafa Hukumar raya yankin Arewa maso Gabas zai zamo daya daga cikin kyawawan abubuwan tarihi da Gwamnati Buhari zata bari a Wannan yanki na Arewa maso Gabas, kuma yayi maraba da batun amincewa da gina hanyar kirfi zuwa Gombe _ Abba da akayi a kwana nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: