Hukumar NITDA Ta Fara Ba Da Horo Kan Noman Zamani Ga Matasa 100 A Jihar Jigawa


Daga Idris Kililin


Bayan kammala horar da manoma 100 akan ilimin noman zamani, wanda aka fi sani da “National Adopted Village for Smart Agriculture” (NAVSA), a ƙarshen makon jiya a Jihar Ogun tare da raba musu kayan aiki.

Hukumar NITDA ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, ta kaddamar ta fara horar da wasu manoma ɗarin a Jihar Jigawa, ranar Litinin, 28 ga watan Fabarairu, shekarar 2022.

Horon wanda ake gudanar da shi a ma’aikatar horar da ma’aikata ta Jihar Jigawa, “Manpower Development Institute, ,(MDI, Dutse), bayan kammala shi za a ba da tallafin kuɗin noma da kayan aiki ga manoman domin inganta ayyuka.

NITDA da ke bisa kulawar ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin zamani, ƙarƙashin jagorancin Shaik, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, ta bijiro da wannan shiri ne domin zamanantar da noma gami da fatan bunƙasa tattalin arziƙin zamani, inda sannu a hankali ta ke aiwatar da shi a Jihohi daban-daban a ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: