Hukumar Marayu da Marasa Galihu (BASOVCA) Ta yaye Dalibanta

Daga Amina Abdullahi Girbo Bauchi

Gwamnatin jiha ta bada Tabbacin shirin ta na gyara Kwalejin koyar da sana o’I da fasahar kere kere ta marayu don samar da kyakkyawar yanayi koyon illimi ga yara marasa galihu.

Shugabar hukumar kula da rayuwar marayu da sauran yara marasa galihu ta jiha BASOVCA, Hajiya Yelwa Abubakar T/Balewa itace ta fadi hakan a wuri liyafar ban kwana da aka shirya wa shugabar Kwalejin mai barin gado Hajiya Asma’u shehu da kuma bikin yaye Dalibai da aka yi a zauren taro na Kwalejin dake nan Bauchi.

Hajiya Yelwa T/Balewa tace Gwamnatin jiha tana bada fifiko ga kyautata walwalar yara marasa galihu,tare da kiran goyon baya daga Wurin masu ruwa da tsaki don cimma manufar da aka sanya gaba

A cewar ta hukumar BASOVCA da ma’aikatar aiyuka da gidaje ta jiha, sun tuntubi hukumomin da abin ya shafa dasu gyara Kwalejin harma da gyaran wasu rijiyoyin burtsatse da suka lalace don kyautata koyon illimi ga Dalibai.

Ta lissafa wasu nasarorin da Kwalejin ta cimma da suka hada da inganta Nagarta Abinci da yawan Abincin, da Dakunan kwanan Dalibai da gadaje da katifun da sauransu.

A yayin da take yabawa gudumuwar da shugabar Kwalejin mai barin gado ta bayar ga Kwalejin koyar da sana o’i ga marayu, Shugabar hukumar BASOVCA tayi wa daliban fatan samun nasara a rayuwa.

Ta kuma yi kira ga daliban da aka yaye dasu cigaba da neman illimi domin su zamo kyawawn jakadun hukumar BASOVCA a duk inda suka samu kansu.

Tun farko shugabar Kwalejin mai barin gado Hajiya Asma’u shehu ta godewa Allah bisa cimma nasarar shafe tsawon shekaru 35 a bakin aiki, kuma ta godewa hukumar gudanar da BASOVCA bisa shirya wannan liyafar don karrama ta, da kuma goyon bayan da suka bata a lokacin da take bakin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: