Hukumar Kula Da Aikin Hajji Ta Kasa (NAHCON) Ta Baiwa Jihar Yobe Kujeru 1,960 A Hajjin 2024

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta baiwa hukumar Alhazai ta jihar Yobe kujeru 1,960 na aikin Hajjin shekara mai zuwa ta 2024.

Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar Yobe Mai Aliyu usman ne ya bayyana haka ya yin da yake zantawa da manyan Jami’an Hukumar da masu karbar kudin shiga na Kananan Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki na hukumar a dakin taro na Hukumar ta Alhazai a garin Damaturu.

Shugaban Hukumar ya shawarci wadanda suka yi ajiya na aikin Hajjin mai zuwa na 2024 da su tabbatar da cewa kudaden da suka ajiye na aikin Hajji ya kai Naira miliyan 3,500,000,00 kafin a yi kididdigewa da kuma sanar da kudaden aikin Hajjin 2024 na karshe daga Hukumar NAHCON.

Mai Aliyu ya bayyana cewa, saboda abubuwan da suke faruwa a halin yanzu, ana hasashen farashin aikin Hajjin bana zai haura sama da hakan.

Don haka ya jaddada bukatar maniyyata su cika ajiyar adadin da aka ambata kana su kuma jira sanarwar karshe na kudin Hajjin 2024 da NAHCON za ta fitar nan bada jimawa ba in Allah Ya so.

Ya ci gaba da cewa, ana sa ran za a fara shirye-shiryen tunkarar aikin hajjin badi na 2024 nan ba da jimawa duk da cewar ko ya zuwa yanzu mai niyyar tafiya aikin hajjin shekarar 2024 ya kawo ajiyar sa za’a karba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: