Hon. Kabir Bichi Ya Samar Da DAM A Malikawar Garu Don Habbaka harkar Noman Rani


Daga Aliyu Dangida


Dan majalisa tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi (FoE) ya samar da katafaren dam a garin Malikawar Garu domin habbaka harkar noman rani a karamar hukumar ta Bichi.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Jamilu Halliru Master, Babban Daraktan Yada Labarai da Hulda da ‘Yan Jarida Na Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, yace
wanna Dam an kashe zunzurutun kudi sama da Naira Miliyan dubu biyu wajen samar da shi.

Dan majalisa wanda sanarwa ta bayyana a matsayin jagora jam’iyar APC na karamar hukumar Bichi ya maida hankali kacokam wajen inganta harkar noman a karamar hukumar Bichi, inda ya samar da takin zamani kyauta ga manoman yankin.

Engr. Abubakar Kabir
ya kuma samar da injinan ban ruwa, da maganin feshi, ga manoma, tare da yi kira ga manoman karamar hukumar Bichi da kungiyoyin manoma da su jajirce wajen ganin an samu isasshen abinci a wannan damuna musamman bisa la’akari da yadda damunar ta yi albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: