Hisbah Da Matasa Sunyi Arangama’ a Unguwar Sabon Gari Kano

Daga Shafin Labaran Hausa


Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya na cewa lamura sun lafa bayan barkewar yamutsi a unguwar Sabon Gari lokacin da jami’an hukumar Hisbah suka kai samame a wani shago da ake zargin ana sayar da barasa.

Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, wanda ya je unguwar ya rawaito cewa lamarin ya faru ne tun da misalin karfe 9 na daren Laraba.

Rahotanni sun ce matasa sun kona tayoyi yayin da aka jibge jami’an tsaro a yankin.

A cewarsa hatsaniya ta kaure ne tsakanin mutumin da jami’an hukumar Hisba suka je shagonsa domin kwace katon-katon na barasar da ake zargin yana sayarwa.

“Hatsaniyar ta fara ne lokacin da jami’an hukumar Hisba suka yi yunkurin tafiya da matar mutumin wadda ke da juna biyu, to a nan ‘yan uwansa suka taso suka ce ba za su bari a tafi da shi ko matarsa ba.

Bayan aukuwar lamarin da na zagaya unguwar Sabon Gari na ga yadda aka kona tayoyi a kan tituna an kuma jibge jami’an tsaro a hanyoyin da za su kai mutum unguwar,” in ji Dokaji.

Lamar in dai ya faru a kusa da kasuwannin da ke Sabon Garin, amma babu wani rahoto daga jami’an tsaro da ke nuna cewa an rasa rayuka.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kano, da hukumar Hisba ba su ce komai a kan rikicin ba.

Sai dai shugaban karamar hukumar Fagge Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi ya shaida wa BBC cewa kura ta lafa, kuma hankula sun kwanta.

“Sabon Gari babu wata matsala ko rigingimu, an kuma girke jami’an tsaro kusan motoci talatin, gobarar da ta tashi tuni ‘yan kwana-kwana sun kashe ta. Babu wanda ya rasu ko jikkata, amma ba mu san takamaimai mutane nawa ne jami’an tsaro suka kama”, in ji Alhaji Ibrahim.

Ba wannan ne karon farko da hukumar Hisba ta Jihar Kano take ƙwace barasa daga masu sayarwa ba, inda take shiga lungu da sako na birnin da ma kauyuka domin kwace barasa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen fara bukukuwan Kirsimati da na sabuwar shekara, lokutan da aka yi amanna cewa ana amfani da shi wajen holewa da kwankwadar barasa da dangoginta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: