Hada Musulmi Da Musulmi Takara A APC Ba Matsala Ba Ne

Daga BBC Hausa

Wasu magoya bayan jam`iyyar APC sun jaddada cewa babu wata illa tattare da matakin da jam`iyyar ta dauka na hada Musulmi da Musulmi a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa.

Magoya bayan na mayar da martani ne ga tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mista Babachir Lawan, wanda ya ce APC ba za ta yi nasara a zaben shugaban kasa ba, tun da ba ta hada Musulmi da Kirista a takarar ba.

Alhaji Akilu Abdullahi Sidi shi ne  shugaban reshen birnin tarayya, Abuja, na kungiyar magoya bayan dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu,  Jagaba For All Movement,  kuma ya shaida wa BBC cewa  maganar Babachir din soki-burutsu ne kawai:

‘’Mu a siyasa ba mu dauki wannan a matsayin wata matsala ba, saboda siyasa mun dauka ta ‘yan Najeriya ce kuma don ci-gaban Najeriya kuma abin da dan takararmu zai kawo ci-gaba ne na kasar nan  da shi da mataimakinsa.‘’

‘’Saboda haka mu ba ma maganar adini a cikin  tafiyar da ake yi . To amma shi tun da ya dauki addini ne, zai yi amfani da shi saboda neman mukami ko wani abu, to ya riga ya makara.’’ In ji shi.

Toh sai dai tsohon sakataren gwamnatin tarrayar ya  yi ikirarin cewa Kiristoci da dama a arewacin kasar ba su ji dadin wannan matakin da jamiyyar APC ta dauka ba na tsayar da Musulmi da Musulmi dan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa ba.

To amma bangaren Bola Ahmed Tinubu ya ce  Mista Babachir na surutu ne kawai don yana neman mukami kamar yadda Alhaji Sidi ya bayanna:

 ‘’To ai ni ban taba sanin Babachir a matsayin fasto ba, mun san ba ya magana da yawun kungiyar Kiristoci ta kasa.”

”Saboda  haka Babachir yana neman mukami ne kuma yana ganin cewa za a dauki mataimakin shugaban kasa a ba shi a kyauta kamar yadda Shugaba Buhari ya ba shi mukamin sakataren gwamnatin tarayya.’’ In ji Alhaji Abdullahi Sidi.

‘’Shi  mutum zai iya musantawa amma kuma bisa ga abin da yake yi, in ba haka ba ba shi kadai ba ne Kirista a Najeriya ba amma mai ya sa ya fito ya nuna abin ya yi masa zafi a siyasan ce.’’

Bangaren Tinubun ya kuma yi ikirarin cewa tare da Babachir ne aka yi yawon neman zaben Bola Tinubu tun kafin a yi zaben fid da gwani.

Sun kuma nuna cewa wannan ya nuna Babachir ba cikakken dan siyasa ba ne saboda ya kasa daukar matakin warware rikicin nasu na cikin gida.

Ya kuma kara da cewa jam’iyyar ta dauki wannan mataki bayan ta tuntubi jiga- jiganta da kuma sauran masu ruwa tsaki a harkar zabenta.

 ‘’Ya nuna cewa shi ba ma dan siyasa ba ne, ai tun daga lokacin da aka tsayar da mutum ya zama dan takara cikakke na jam’iyya kuma  zai wakilici  jam’iyyarsa.

‘’Tinubu bai isa ya zabi mataimakin shugaban kasa ba, sai an hada da jam’iyya  an  tattauna da juna, an tabbatar da cewa ga wanda ya cancanta ya mara masa baya da za su yi aiki tare  su kawo wa Najeriya ci-gaba’’ in ji Alhaji Nasidi.

Toh sai dai kuma wasu na ganin barakar da ta kunno kai za ta iya kawo cikas ga  jam’iyyar ta APC mai mulki a zaben da ke tafe ko da yake  bangaren Bola Tinubu ya ce wannan barazanar da suke fuskanta daga wurin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ba za ta yi tasiri ba.

‘’Ai ba mu taba daukar Babachir a matsayin wani jigo ba saboda tun daga ranar da aka koreshi da ga mukaminsa na SGF mu dai ba mu san wani zabe da aka yi  ko a Adamawa nashi wanda Babachir ya yi rawar gani ba. Ko a ward dinsa ma ba ya kawowa’’ In ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: