Gwamnatin Kaduna Ta Kashe Kasurgumin Dan Bindiga

Daga BBC Hausa

Gwamnatin jihar Kaduna, a Najeriya, ta ce ta tabbatar da kashe wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ya yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare da satar mutane a yankunan Kajuru da Kachia da Chikun.

Gwamnatin ta ce an kashe Kachallah Gudau ne bayan wani yunƙuri da mayaƙansa suka yi a ƙarshen mako na kai farmaki kan sojin Najeriya da suka hana su sakat a baya-bayan nan.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro a jihar ta Kaduna, Samuel Aruwan ya yi wa BBC ƙarin bayani game da wannan nasara da dakarun tsaron kasar suka ce sun samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: