Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar da Rabon Kayan Awon Cuta mai Karya Garkuwar Jiki (HIV)
Daga Aliyu Dangida
Kwamishinan ma’aikatar lafiya na Jihar Katsina, Dr. Bishir Gambo Saulawa ya wakilci mai girma Gwamnan Jihar Katsina Dr. Dikko Umar Raɗɗa wajen kaddamar da rabon kayan awon cuta mai karya garkuwar jiki HIV ga cibiyoyin awo dake faɗin jihar Katsina.
Kayayyaki wanda hukumar yaki da cutar sida ta jihar Katsina ta kaddamar da raba kayan awon cutar sama da dubu uku a asibitocin dake faɗin Jihar Katsina a ƙarƙashin Jagorancin shugaban hukumar Dr. Bala Nuhu a ofishin hukumar.
Yayin kaddamar da rabon kayan awon ƙwamishinan lafiya na Jihar Katsina Dr. Bishir Gambo Saulawa wanda ya samu wakiltar mai girma Gwamna ya bayyana wasu daga muhimman tsare tsare na cigaba da Gwamnatin Jihar Katsina a ƙarƙashin Jagorancin Dr. Dikko Umar Raɗɗa take shiryawa wanda za su taimakawa ɓangaren kiwon lafiya a Jihar Katsina domin kawo cigaba da al’umma za suyi alfahari.
Dr. Bishir Gambo Saulawa ya ƙara bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina tayi shiri na musamman na shigowa da sabbin tsare-tsare na amfani da sabbin kayan aikin awo cututuka na zamani a asibitocin Jihar Katsina.
Daga ƙarshe yayi alƙawarin cigaba da zage damtse wajen ganin cewa ɓangaren kiwon lafiyar Jihar Katsina ya inganta a kowane fannin.
*Kwafowa Daga Shafin Mustapha Rabi’u Garkuwa.