Gwamnati Ta Umurci Ma’aikata Su Zauna A Gida a Bayelsa

Daga BBC Hausa

Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya umurci daukacin ma’aikata a jihar da su zauna a gida na tsawon mako daya ban da ma’aikata masu ayyuka na musamman domin takaita barazanar ambaliya da take shafar al’ummomi.

Gwamnan ya bayar da umurnin ne yayin wani jawabi ga ‘yan jihar baki daya a kafofin yaɗa labarai a yau Talata.

Diri ya ce ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita al’ummomi da dama a jihar wanda kuma ya jefa rayuwar magidanta cikin mawuyacin hali.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa ruwa ya mamaye wani bangare na sakatariyar jihar da ke Yenagoa.

Ya bukaci masu sayar da kayaki kamar man fetur da abinci da ruwa da kuma magani da kada su yi amfani da yanayin wajen kara farashin kayaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: