Gwamna Matawalle Ya Bada Gudumawar Naira Milyan 100 Don Gina Jami`ar Musulunci

Daga Anas Funtua, Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya bada gudunmawar Naira milyan 100 ga qungiyar izala (JIBWIS) ta qasa don taimakawa niyyar su wajen aikin gina jami`ar musulunci a jihar Jigawa.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin mai taimakawa na musaman ga gwamnan shawara a kan harkokin yaxa labarai da sadarwa, Zailani Baffa ta ruwaito cewar gwamna Matawalle ya sanarda bada gudunmawar kuxin ne yayin da shugabancin qungiyar Izala qarqashin jagorancin, Sheikh Bala Lau suka kai masa ziyara a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau. Gwamna Matawalle ya ce bada gudunmawa don bunqasa al`amurran ilmi abu ne mai muhimmanci musamman ilmin addinin musulunci, inda yayi kira ga sauran gwamnoni da sauran masu hannu da shuni da su taimaka wa wannan muhimmin aiki da qungiyar ta xauko na bunqasa ilimin addinin musulunci, ya qara da cewa qungiyar Izala, qungiya ce mai gaskiya da riqon amana wadda take da shugabanci masu aiki tsakanin su da Allah don ciyar da qasa gab .

Ya qara da cewa matsalar masu satar shanu da masu garkuwa da mutane don neman kuxin fansa ya na neman zama ruwan dare a wannan yankin inda ya danganta matsalar da rashin son juna a tsakanin `yan arewa. “A yau za ka ga mun sa qiyayyar junan mu a zukatanmu, mun bai wa wasu mutane masu son kansu muhimmanci don cimma burin su.” A cewar Matawalle.

Ya ce mutanen yankin bas a qaunar junan su don haka sun fifita vata garin mutane a cikin al`umma, “Na yi iya bakin qoqarina wajen samar da zaman lafiya mai xorewa, kuma b azan gaza wajen cimma wannan buri nawa ba don ceto al`umma daga mummunan yanayi da suka tsinci kansu”.

“A matsayin ku na malamai ya zama wajibi ku qara qaimi wajen gani cewar al`umma sun ilmantu saboda ilmi shine ginshiqin rayuwa”. Matawalle ya sanarda shugabancin qungiyar.

Da yake jawabi, shugaban qungiyar Izala na qasa, Sheikh Bala Lau ya faxawa gwamna Matawalle cewar ya jagoranci tawagar ne don su duba makaranta da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya sadaukar wa da qungiyar a matsayin gudunmawa a garin Shinkafi ta jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: