Gwamna Buni Ya Yabawa Gwamnatin Tarayya Kan Maido Kudaden Ta A Matsayin Diyya Na Hanyoyi Da Ta Gina

 Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yabawa gwamnatin tarayya bisa amincewar da maido da makudan kudi kimanin Naira biliyan 18 da gwamnatin jihar ta kashe wajen sake gina titunan gwamnatin tarayya guda biyar da ke jihar.

Gwamna Buni ya yi wannan yabon ne bayan amincewar da majalisar zartarwa ta tarayya ta yi na mayar wa gwamnatin jihar kudaden, ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi amfani da kudaden cikin adalci wajen samar da karin ababen more rayuwa a yawancin al’umma a fadin jihar.

 .

“A cewarsa, mayar da kudaden zai bai wa gwamnatin jihar damar gudanar da wasu ayyuka da suka shafi jama’a da za su inganta rayuwar al’umma. 

“Ina so in yaba wa shugaban kasa musamman da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya bisa yadda suke nuna adalci ga jihar. 

“Alal hakika samun wadannan makudan  kudaden zai ba da gudummawa ga sauran ayyukan da za su yi tasiri ga rayuwar mutanenmu.

“Gwamnati za ta karkatar da albarkatun zuwa ilimi, samar da kiwon lafiya, samar da ruwan sha, samar da ayyukan yi da sauran ababen more rayuwa domin inganta rayuwar al’ummar mu”. Gwamna Buni. 

Ya bayyana cewa irin wannan fahimtar da ke tsakanin gwamnatocin Jihohi da na tarayya za ta sa gwamnatin jihar za ta kara kaimi wajen aiwatar da ayyukan gwamnatin tarayya da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.

Mahangar Arewa ta ruwaito cewar Majalisar zartaswa ta tarayya a zamanta karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta amince wa gwamnatin jihar Yobe Naira biliyan 18 dangane sake gina  wasu hanyoyin gwamnatin tarayya guda biyar da gwamnatin jihar ta sake ginawa tuntunin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: