Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Bada Tallafin Naira Miliyan 100 a Garin Nguru

 Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya kaddamar da shirin  bada tallafin Naira miliyan 100 da jari ga wasu Matasa 100 a garin Nguru Hedikwatar  Karamar Hukumar Nguru a jihar Yobe. 

Yayin da yake jawabi, Gwamnan ya yabawa Wanda ya bada wannan dangane da irin kwazon da ya nuna wajen bada wannan  taimakon ga matasa don su tsaya da kafafun su na zunzurutun kudi har Naira Miliyan 100  ga matasa dari. 

Tun da farko mai bayar da tallafin, Alhaji Balarabe Abdullahi ya ce ya yanke shawarar taimakawa matasa dari da Naira Miliyan daya kowannensu don fara kasuwanci a wani bangare na tallafin da yake baiwa gwamnatin jihar.

Don haka Alhaji Balarabe ya yi fatan Matasan za su bi hanyoyin da suka dace wajen gudanar da harkokin su na kasuwanci ta yadda nan gaba su ma za su yi koyi da haka. 

Kana ya kuma kirayi masu hannu da shuni da kuma daidai kun al’umma da su taimaka wajen talllawa Matasan mu don ganin sun zama nagari cikin al’umma wadda ta yin haka ne kadai Za’a rage matsalolin da ake fuskanta a yanzu han harkokin tsaro. 

Daga nan ne sai gwamna Buni Ya Gabatar da cak na Naira Miliyan guda ga kowane daya daga cikin. Matasan tare da musu gargadin da su yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace musamman don haɓaka harkokin kasuwacin su kamar yadda maanufar shirin ya nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: