Gwamna Buni Ya Gargadi Sabbin Shugabannin Riko Na Kananan Hukumomi Da Su Yi Aiki Da Gaskiya Da Rikon Amana

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, gargadi sabbin Shugabanni riko na kananan hukumomin Jihar 17 da su yi aiki da gaskiya tare da Rikon Amana A ga al’ummomin da za su jagorantar.

Gwamnan ya yi wannan gargadi ne a jawabinsa wajen Rantsar da shugabannin Rikon da aka gudanar a dakin taro da ke gidan gwamnatin Jihar a Damaturu.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta hada kai da kananan hukumomin jihar kan shirye-shirye da ayyukan da suka shafi rayuwar al’ummarta kai tsaye.

Shugabannin kwamitin sun hada da Alhaji Ibrahim Babagana- Bade Local Government, Lawan Bukar-Bursari, Bukar Adamu-Damaturu, Hajiya Halima Kyari joda-Fika, Baba Goni Mustapha-Fune, Musa Mohammed-Geidam da Dala Mala-Gujba,

Sauran sun hada da Dayyabu Ilu-Gulani, Umar Abba-Jakusko, Khalid Abba Umaru-Karasuwa sai Bukar A Bukar-Machina, Alhaji Salisu Yerima-Nangere da Alhaji Modu Kachalla na karamar hukumar Nguru.

Akwai kuma Salisu Mukhtari karamar hukumar Potiskum, Mohammed Lamido Musa-Tarmuwa, Zannah Zakariya kalgi-Yunusari, da Alhaji Waziri Ibrahim, karamar hukumar Yusufari.

Gwamna Buni ya kuma shawarci sabbin shugabannin kwamitocin da aka rantsar da su bi tsarin da ya dace da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu domin samun sakamako mai kyau.

Ya kuma bukace su da su kasance masu himma da rikon amana wajen tafiyar da abubuwan da Suka shafi jagorancin a’ummomin su bi-hakki da gaskiya don samun ingantacciyar fa’ida wajen inganta rayuwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: