Gwamna Buni Da Zababbun ‘Yan Majalisun Sun Karbi Takardar Shaidar Cin Zabe Daga INEC

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu


Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da zababbun ‘yan majalisar jihar sun karbi takardar shedar lashe zabe daga INEC a Damaturu ranar Laraba bayan zaben da suka yi a ranar 18 ga watan Maris.

A jawabinsa na karbar, Buni ya yabawa al’ummar Yobe bisa yadda suka gudanar da zabe cikin lumana a lokacin zaben.

“Abin farin ciki ne cewa mu mutanen Yobe mun gudanar da zabukan mu cikin lumana da Sanin ya kamata a duk zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

“Hakika mun tabbatar da cewar, Jihar Yobe Jiha ce da ake gudanar da zabe na lumana bisa ga manufar ‘Siyasa Ba da gaba ba’ kamar yadda fitaccen dan siyasarmu, Marigayi Alhaji Waziri Ibrahim ke fada a baya” inji shi.

Alhaji Ibrahim waziri shi ne ya kafa jam’iyyar Great Nigeria Peoples Party (GNPP) ta rusasshiyar jamhuriya ta biyu.

“Har ila yau, abin farin ciki ne yadda ’yan siyasa da magoya bayansu a jihar suka ki ba da damar rikicin siyasa da ‘yan daba da ya samu gindin zama.”

“Hakan ya kara sanya jihar Yobe ta zama abin koyi wajen gudanar da zabe cikin lumana domin sauran jihohin su kwafa.” Buni ya kara da cewa.”

“Ina kuma so in yaba wa jam’iyyun siyasa na adawa da ‘yan takararsu bisa nuna sha’awa da sha’awar yi wa jiharmu hidima ta hanyar siyasa mai kyau,” in ji shi.

Buni ya nuna cewar, kofar sa, a bude ta ke ga kowane dan Jihar don ganin an bada gudummawa wajen gina jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: