Gwamna Bala ya gargadi shugabanni su kara himmatuwa wajen Inganta tsaro a Jihar Bauchi

Daga Mu`azu Hardawa

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, yayi gargadi shugabannin kananan hukumomi da na tsaro da kuma ‘yan siyasa game da inganta tsaro da kare martabar gandun daji a Jihar Bauchi.

Gwamnan yayi wannan gargadi ne a lokacin taro kan sha’anin tsaro wanda ya gudana tare da shugabannin hukumomin tsaro da manyan jami’an gwamnati da shugabannin kananan hukumomi a gidan gwamnatln Bauchi.

Gwamna Bala, cikin jawabinsa ya ja kunnen jami’an kananan hukumomi da sarakuna kan kauracewa jefa kansu cikin matsalar lalata gandun daji da goyon bayan masu aikata laifuka inda ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi hukunci mai tsanani ga duk wanda ta samu da hannu a wannan badakala.

Yace kutse da ake yiwa gandun dajin gwamnati, yana daya daga cikin manyan matsalolin da ke jawo rikici a kasa, don haka ya umarci dukkanin su kan su dauki matakin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta.

Sanata Bala ya kuma umarci shuwagabannin kan su rika gudanar da taro kan sha’anin tsaro lokaci zuwa lokaci da shugabannin al’u’mma, da ‘yan Banga domin tabbatar da samar da kyakkyawan tsari akan sha’anin tsaron yankunan su.

Gwamnan wanda yace shigo da al’uma cikin al’amuran tsaro shine hanyar da za ta kara karfafa tsaro, don haka ya bada tabbacin goyon bayan gwamnatinsa domin cimma abubuwan da aka sanya a gaba wajen inganta zamantakewa da tsaro saboda a ciyar da kasa gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: