Gwamna Badaru Ya Mika sakon Ta’aziyya ga Iyalan Salisu Zakar

Daga Aliyu Dangida

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Alhaji Salisu Zakar kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Jigawa.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Salisu Zakar ya yi aiki a jihar Jigawa a mukamai daban-daban, tun daga ma’aikacin gwamnati, ya zama shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (SUBEB), sannan kuma ya zama kwamishinan kasuwanci da masana’antu.

A wata sanarwa mai dauke da da hannun Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Auwal D. Sankara (FICA), tace Salisu Zakar

Ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano, da ke jihar Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.

A cewar Gwamnan, Alhaji Salisu Zakar mutum ne wanda ya yiwa Jigawa hidima da gaskiya da rikon amana, kuma ya kasance daya daga cikin nasarorin da gwamnatin ta samu.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya jikan marigayin da Jannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba.

Marigayin wanda dan asalin garin Hadejia ne kuma Mai rike da sarautar gargajiya ta Chigarin Hadejia, za a gudanar da jana’idarsa a fadar mai martaba Sarkin Hadejia da karfe 11 na safiyar asabar kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: