Gwamna Badaru Ya Jajantawa Wanda Ambaliya Ta Shafa

Daga Aliyu Dangida

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya jajantawa wadanda Ambaliyar ruwa ta shafa a fadin jihar Jigawa da suka hada da babban birnin jihar.

Gwamnan a wata sanarwa da kwamishinan ayyuka na musamman, Auwal Danladi Sankara ya sanyawa hannu tare da rabawa manema labarai a Dutse, ya ce an dauki ambaliya a matsayin hanyar da Ubangiji yake gwada bayinsa.

A cewar sanarwar, kusan dukkanin kananan hukumomin jihar ambaliyar ta shafe su, inda wasu daga cikin kananan hukumomin suka yi rahoton mutuwar mutane da jikkata da dama.

“Ina so in yi amfani da wannan dama domin jajantawa al’ummar jihar Jigawa tare da jajanta wa wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa da aka shafe sama da sa’o’i talatin anayi.” Gwamnan ya ce a cikin wata sanarwa.

Ya kara da cewa, “Tasirin sauyin yanayi wani lamari ne da bai bar kowane bangare na duniya ba. A bara mun fuskanci karancin ruwan sama amma bana ya sha bamban. Wannan ita ce hanyar Allah ta jarrabar mu.”

“Daga rahoton, mun sami labarin mutane shida da suka rasa rayukansu, uku a Kirikasamma, uku kuma a karamar hukumar Kafinhausa ta jihar.

Ina amfani da wannan kafar wajen mika ta’aziyyata ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da yi musu addu’ar Allah ya ba su Jannatul Firdausi.” Gwamnan ya kara da cewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: