Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singa Da Ke Kano
Daga Mujtaba Gali
Gobara ta tashi a kasuwar kayan masarufi ta Singa da ke Kano a arewacin Najeriya.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin wutar ba, to sai dai wani mai shago a kasuwar ya shaida wa BBC cewa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar
Kawo yanzu wutar na ci , yayin da jami’an kashe gobara ke kokarin shawo kan wutar.