Gasar Kofin Duniya: Neymar Ba Zai Buga Wasa Biyu Ba

Daga Mujtaba Gali

Likitan tawagar ƙwallon ƙafa ta Brazil ya ce fitaccen ɗan wasan tawagar ƙasar Neymar ba zai buga karawa biyu da suka rage na cikin rukuni ba, sakamakon raunin da ya ji a idon sawu.

An cire ɗan wasan mai shekara 30 a minti na 80 a fafatawar da ƙasar ta ci Serbiya da ci 2-0.

Ɗan wasan ya bayyana raunin da ya ji a matsayin ‘ɗaya daga cikin abu mafi wahala a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa’

“Babu abin da ya zo min da sauƙi a rayuwata a kodayaushe ina ƙoƙarin cimma burina na cin ƙwallaye ”, kamar yadda ɗan wasan ya rubuta a shafinsa na Instagram.

“Ban taɓa yi wa wani mummunan fata ba, a kullum ina taimakon mai buƙatar taimakona”.

”Na ji rauni, haƙiƙa babu daɗi, to amma ina da tabbacin cewa zan samu sauki domin dawowa fili, zan yi duk mai yiyuwa domin taimaka wa ƙasata, da abokan wasana, da kuma kaina”.

Dan wasan na PSG ya sha fama da jinyar idon sawu a ƙafarsa ta dama a ‘yan shekarun da suka gabata.

A shekarar 2019 ma bai buga gasar Copa America ba, bayan da ya ji irin wannan ciwon, haka kuma a shekarar 2021 ma ya kwashe makonni yana fama da irin wannan jinya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: